Biya 20,000 a baka 15,000: Bankuna sun fara karɓar na goro kafin su canja sabbin kuɗi
Biya 20,000 a baka 15,000: Bankuna sun fara karɓar na goro kafin su canja sabbin kuɗi.
Wasu ma’aikatan Bankuna kasuwanci na Najeriya sun fara karɓar cin hanci kafin su canja wa jama’a, sabbin takardun Naira
Wasu ‘yan kasuwa a babbar kasuwar garin Onitsha (Onitsha main market) dake jihar Anambra, sun koka cewa ma’aikatan Bankuna dake kasuwar suna canja kuɗin ne kawai ga duk wanda ya basu cin hanci.
Jaridar Business Day ta ruwaito cewa, ‘yan kasuwar sun bayyana adawar su da tsarin ne lokacin da kwanturola na babban bankin Najeriya (CBN), a Onitsha, Benedict Maduagwu ya shiga kasuwar domin ci gaba da wayar da kan ‘yan kasuwa gameda muhimmancin canja takardun Nairar akan lokaci.
Shugaban ‘yan kasuwar ta Onitsha main market, Mista Innocent Ezeoha, ya shaidawa kwanturolan bankin na CBN cewa، idan har da gaske suke to jami’an bankin na CBN su shigo kasuwar da kansu da sabbin takardun Nairar su canja wa jama’a.
Ya ce halin da ake ciki yanzu ma’aikatan bankunan kasuwanci su mayar da canja takardun Nairar wata kafa ta cin hanci da rashawa.
“Sun ma kayyade nawa mutum zai biya, idan kana son canja dubu goma sha biyar misali, to Naira dubu ashirin za ka biya” a cewar mista Innocent Ezeoha.
Source: https://gaskiyatafikwabo.com
0 Response to "Biya 20,000 a baka 15,000: Bankuna sun fara karɓar na goro kafin su canja sabbin kuɗi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?