Allahu Akbar. Cikakken abinda ya faru da Muneerat Abdussalam
Wednesday, 26 October 2022
Comment
Nayi Damar Karuwanci Da Irin Barikin Da Nai A Baya ~ A Cewar Muneerat Abdulsalam Bayan Tasha Dukan Tsiya A Wurin Saurayinta
Sananniyar Mai amfani da kafafen sadarwa tana furta kalaman batsa, da baɗala Muneerat Abdulsalam tace tayi Nadamar abubuwan da ta aikata a rayuwar ta.
Jarumar ta bayyana cewa tayi wani saurayin da suke ƙoƙarin yin Aure amma kuma daga baya ta fahimci cewa bayada halaye masu kyau a dan haka ta gudu ta rabu dashi, daga baya ya ganota yakuma lakaɗama ta duka.
Ga saƙon vidio da ta saki a Shafin ta na Facebook👇
A baya dai Muneerat ta kan Naɗi faifan Bidiyo da kalaman ɓatsa da sunan saida Maganin gyaran Maza ko na Mata, lamarin da yasanya jama'a ke ganin abinda take ya saɓa ma ƙa'ida harma akaita taƙaddama da ita, wani lokaci ma tace ta bar Musulinci kafin daga baya ta dawo.
Yanzu haka ta shiga kunci da tsananin rayuwa komai ya tsaya mata a cewar ta.
Wane fata zaku yi mata?
0 Response to "Allahu Akbar. Cikakken abinda ya faru da Muneerat Abdussalam"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?