Zaben 2023: Shekarau, Barau Da Kawu Sumaila Na Shirin Ficewa Daga APC zuwa NNPP Kwankwasiyya
Zaben 2023: Shekarau, Barau Da Kawu Sumaila Na Shirin Ficewa Daga APC zuwa NNPP Kwankwasiyya
Biyo bayan matakin da Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC ta jihar Kano suka yanke a wani taro da aka gabatar a fadar gwamnatin Kano ranar Lahadi, yasa wasu cikin Jigajigan Jam’iyyar APC a Kano tunanin sauya sheka zuwa NNPP.
A zaman an amince wa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya nemi takarar Sanatan Kano ta Arewa ba hamayya, a Kano ta tsakiya kuma Shekarau bai samu tikitin takarar kai-tsaye ba.
Jam’iyyar APC ta ce Sanata Shekarau din zai shiga zaben cikin gida tare da tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Bashir Garba Lado.
Wata majiya daga bangaren Sanata Shekarau data bukaci a sakaya suna, ta ce duba da makarkashiyar da gwamnatin ki shirin yi masa a zaben fidda gwanin, shi yasa Shekarau din ya yanke shawarar ficewa daga Jam’iyyar zuwa NNPP ta Sanata Kwankwaso don yin takarar Sanata a Jam’iyyar.
Hukuncin da Jam’iyyar ta yanke kan Shekarau din kusan shi ne dai ta yanke akan takarar Sanatan Kano ta kudu da Kawu Sumaila me nema, inda alamu ke nuna abokin karawar tasa Sanata Gaya na da goyan bayan gwamnati don haka shima ya yanke hukuncin dira cikin NNPP.
BARAU, Matakin amincewa Ganduje takarar Sanatan Arewacin Kanon na kunshe cikin yarjejeniyar da masu ruwa da tsakin Jam’iyyar APC suka cimma a zaman nasu.
Majiyarmu ta jiyo cewa, tuni Barau din ya taba alli da Sanata Kwankwaso kan komawarsa Jam’iyyar NNPP don yin takarar Sanata a kujerar da yake ta Kano ta Arewa da Gandujen ke neman karbewa.
A zaman na ranar Lahadi a fadar gwamnatin Kanon ne aka sahalewa Gawuna da Garo takarar gwamna da mataimaki.
Shi ma mai neman takarar gwamna a APC, Bashir Ishaq Bashir daga tsagin Shekarau, tuni ya sanar da ficewar tasa daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP ta Sanata Kwankwaso a shafinsa na fecebook a ranar Lahadi bayan sanarwar ficewar tsohon Kakakin Majalisar dokokin Kano Rurum.
0 Response to " Zaben 2023: Shekarau, Barau Da Kawu Sumaila Na Shirin Ficewa Daga APC zuwa NNPP Kwankwasiyya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?