‘Yan siyasan Arewa 10 baya ga Atiku, Kwankwaso, da Yarima masu harin zama Shugaban kasa
A rahoton nan da mu ka kawo, mun kawo sunayen wasu daga cikin wadanda suka yanki fam, suka fito neman takarar shugabanci daga Arewacin Najeriya. Bari mu fara da ‘yan jam’iyyar PDP:
1. Atiku Abubakar,Tsohon mataimakin shugaban kasar yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen neman tikitin PDP. A zaben 2019, Wazirin Adamawa ya yi takara, amma ya sha kashi a hannun APC.
2. Bukola Saraki Tsohon shugaban majalisar Najeriya, Bukola Saraki yana cikin wadanda za su shiga zaben fitar da gwani a PDP. Tsohon Gwamnan ya fito ne daga yankin Arewa maso tsakiya.
3. Aminu Waziru Tambuwal Aminu Waziru Tambuwal wanda ya yi shugaban majalisar wakilan tarayyan tsakanin 2011 da 2015 zai tsaya takara kamar yadda ya yi a 2018, shi ne gwamnan Sokoto.
4. Bala Mohammed Shi ma Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed yana cikin ‘yan gaba-gaba a zaben fitar da gwani a PDP. Tsohon Ministan zai jarraba sa’arsa a zabe mai zuwa.
5. Mohammed Hayatu-Deen Mutumin Arewa na karshe da ke takara a jam’iyyar PDP a zaben 2023 shi ne Mohammed Hayatu-Deen. Hayatu-Deen masanin harkar banki da tattali ne daga jihar Borno. Masu neman tikitin Jam’iyyar APC
6. Ahmad Lawan Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan zai tsaya takara bayan an sayo masa fam a makon nan. Akwai masu ganin ya kamata 'Yan Arewa maso gabas su karbi mulki.
7. Mohammed Badaru Abubakar A jerin akwai Mai girma gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar wanda ya zabi ya saye fam din zama shugaban kasa bayan an yi tunanin zai nemi Sanata.
8. Ahmed Sani Yarima Sanata Ahmed Sani Yeriman Bakura, wanda ya yi mulki na shekaru takwas a Zamfara ya ayyana shirin takara. A zaben 2007 Bakura ya nemi zama shugaban kasa a ANPP.
9. Yahaya Bello Tun tuni ake rade-radin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi zai nemi shugaban kasa. ‘Dan siyasar shi ne mutumin Arewa na farko da ya yanki tikiti a jam’iyyar APC mai mulki. Sauran Jam’iyyun hamayya
10. Rabiu Musa Kwankwaso Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya saye fam domin yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP bayan ficewarsa daga PDP a karshen watan Maris.
Source: Legit
0 Response to "‘Yan siyasan Arewa 10 baya ga Atiku, Kwankwaso, da Yarima masu harin zama Shugaban kasa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?