Wata sabuwa Kuma: Dalilai 10 na rashin cancantar Gawuna/Garo -Injin Matashin Lauya Abba Hikima
Dalilai 10 na rashin cancantar Gawuna/Garo
1. Zaben Gawuna a matsayin Gwamna zai karfafa sakawa barna. Ka’ida ce sananniya ga ma’abota hankali da wayewa cewa ba a barin mutum ya amfana da barnar sa. Duk da mun san Allah ne ke gudanar da komai amma a matsayin mu na mutane, zamu iya cewa inda abunda ya faru a unguwar Gama sakamakon abunda Gawuna da Garo suka yi wa mutanen Kano a zaben 2019 bai faru ba, to da Gawuna bai samu damar zama Deputy ba yanzu. Wanda hakan ne ya karfafe shi yanzu wajen samun sahalewar Ganduje kuma kai tsaye yake nuna cewa Gawuna ne dan takarar Gwamna a APC a 2023.
Ko a shari’ance muna da wasu ka’idoji guda biyu masu cike da hikima wanda suke cewa “No one should be allowed to benefit from his own wrongs.” Ma’ana haramun ne a bar wani ya amfana da aikin barna ba. Da kuma “He who comes to equity must come with clean hands.”
Ya kamata su karbi sakamakon su a hannun hagu a zaben 2023. Al jaza’u min jinsil amal.
2. Zaben Gawuna zai iya kare Ganduje daga bincike da dama na zargen-zargen cin hanci da rashawa da ake wa Gandujen. Bayan zargin faifan bidiyon dala wanda duk duniya ta gani, a ranar 25/02/2022 jaridun kasar nan sun rawaito maganar Prof. Sadiq Isa Radda, Shugaban komitin dake bawa shugaban kasa shawara akan yaki da cin hanci da rashawa wato Presidential Advisory Committee On Anti-Corruption (PCACC) inda shuganan na yace “ Ganduje yana da kyasa-kyasai da dama na zarge-zargen cin hanci da rashawa da zai amsa bayan ya bar mulki. Saboda haka ko dan hukumomi su samu damar aiwatar da ayyukan su bai kamata mu zabi dan takarar Ganduje ba saboda akwai yiwuwar ya toshe kofar binciken ko kuma ya kawo wa binciken tasgaro. Dama abune mai kamar wuya ace gwamnatin Gawuna ta tuhumci Ganduje. Magana ake ta hukumomin gwamnatin tarayya kamar su EFCC da ICPC. Saboda haka ko dan a yiwa jama’a da ma shi kansa Gandujen adalci, akwai bukatar samum shugabancin da Ganduje baya bin sa bashi. Wanda zai iya bincikar gandujen akan zarge zargen dake kan sa.
3. Zaben Gawuna zaben Garo ne.
Zaben Gawuna da Garo a matsayin mataimaki na alamta gwamnatin Garo a matsayin Gwamna a 2031. Tunda salon mulkin Kano ya zama daga gwamna sai deputy. Kamar yadda ya faru tsakkanin Kwankwaso da Ganduje. A tunani na Garo bai dace da ko wane irin matsayi na shuganacin al’umma ba, duba da antecedents din sa. Musamman shugabancin kujera ta biyu mafi girma a Kano. Wanda zaben Garo a matsayin mataimakin gwamna zai bashi rigar kariya daga kamu da kuma gurfanarwa a gaban shariah. Kamar yadda kowa ya sani akwai zarge-zarge na cin hanci da rashawa akan Garo shi kan sa. Ana alamta cewar daya daga cikin dalilan da suka sa Goggo (wadda itama akwai zarge-zarge a kan ta da dama musamman wanda dan ta Abdulaziz Ganduje ya zargeta akai) ta ayyana shi Garon a matsayin wanda ya kamata ya gaji mijin ta shine domin ta offishin sa ake wadaka da kudin local government da kuma cewar bashi mulkin kadai ne zai iya rufa asirin wadannan mutane.
In za’a tuna ko a shekarar 2020 jaridu sun rawaito cewa hukumar EFCC ta gayyaci Garo inda wata majiya ta ce an gayyace shi ne akan zargin mallakar kadarori a Kano da Abuja wanda albashin sa bazai iya siya masa ba da kuma zargin siyar da kadarorin kananan hukumomi.
Na tabbata bana bukatar bada hujjoji masu yawa akan rashin cancantar Garo saboda abubuwa a fili suke. Wannan kuma ya hada da rashin gogewar sa, ilimin sa da sauran su.
Mutanen Latin na cewa “Res ipsa loquitur”. Bature kuma na cewa “the fact speaks for itself. “
4. Duba da saukin kai da halin girmama mutane da Gawuna ke da shi, yana da wahala yayi fada da Ganduje bayan zama Gwamna, Idan kuma Gawuna bai yi fada da Ganduje ba bayan zama gwamna to Ganduje zai ci gaba da samun relevance da kariya a siyasance da kuma a aikace a jahar Kano. Sannan Kano bata bukatar Gwamna wanda bazai bawa jami’ai damar da gudun mowar bincikar gwamnatin Ganduje ba. Daga maganar zargin faifan video zuwa wadaka da filaye, zuwa Zarge-zarge da dama da akewa Ganduje a tafiyar da mulkin sa zasu iya bin ruwa idan Gawuna ya zama gwamna.
5. Zaune bata karewa mutan Kano ba. Kuma kimar mu zata ci gaba da yin kasa a idon duniya. Idan muka zabi Gawuna da Garo to zaune bata kare mana ba musamman ta fuskar irin faduwar kimar mutanen Kano. Duk wani mai kishin kan sa bai ji dadin abun da ya samu Kano ba bayan fitar bidiyon dala. Saboda hatta kalmar “babbar-riga” bata taba samun shuhra a kudancin Nigeria ba kamar wannnan lokaci ba. Yanzu yan jamiyyun adawa sun fara kiran Gawuna da Garo da wani suna wanda baza a ji shi a baki na ba, sakamakon abun da ake zargin su biyun da yi a Gama. Jaridu da dama sun labarto wannan abu kuma abune na kaskanci da rashin kyautawa, wanda ko kadan bai kamaci shugaba ba. Shugaba abun misali ne a cikin al’umma. Wannan kuma ba misalin kirki bane kuma ba yadda za’a iya goge shi. Musamman yadda hotuna da bidiyon su ya yadu cikin kaskanci.
Zan ci gaba inshaAllah.
0 Response to "Wata sabuwa Kuma: Dalilai 10 na rashin cancantar Gawuna/Garo -Injin Matashin Lauya Abba Hikima"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?