--
Jonathan Ya Yi Martani Bayan Ƙungiyar Fulani Ta Siya Masa Fom Ɗin Takarar a APC-BZGLOBALSERVICES

Jonathan Ya Yi Martani Bayan Ƙungiyar Fulani Ta Siya Masa Fom Ɗin Takarar a APC-BZGLOBALSERVICES


 Jonathan Ya Yi Martani Bayan Ƙungiyar Fulani Ta Siya Masa Fom Ɗin Takarar a APC


Tsohon shugaban kasar Najeriya Dr Goodluck Ebele Jonathan ya yi watsi da fom din takarar shugaban kasa da kungiyar fulani ta siya masa


Jonathan, ta bakin mashawarcinsa Ikechukwu Eze ya ce bai aike su ba kuma 'cin mutunci' ne a siya fom da sunansa ba tare da neman izininsa ba



Ya kara da cewa har yanzu bai yanke shawarar ce zai amsa kirar magoya bayansa ya shiga takarar ko akasin hakan ba yana mai kira da mutane su yi watsi da siya fom din


Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi watsi da fom ɗin takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progresives Congress, APC, da wata kungiyar magoya bayansa daga arewa suka siya masa, rahoton Daily Trust.



Jaridar The Cable ta ce Ikechukwu Eze, mashawarcin Jonathan a bangaren watsa labarai, ya bayyana hakan awannin bayan labarin cewa an siya masa fom ɗin yana mai cewa ba a nemi izinin tsohon shugaban kasar ba kuma ya dauki shi a matsayin 'cin mutunci'.


"Muna son mu fayyace cewa Dr Jonathan bai san da batun ba kuma bai bada izini ba," wani sashi na sanarwar ta ce.


"Muna son mu bayyana cewa idan tsohon shugaban kasar na son takara zai bayyana niyyarsa ƙarara ga al'umma kuma ba zai shiga ta bayan gida ba."


A baya-bayan nan dai an yi ta kira da Jonathan ya shiga takarar shugaban kasar amma ya umurci magoya bayansa su jira.


"Duk da muna godiya bisa goyon baya da yan Najeriya da dama ke nuna masa ya fito takarar shugaban kasa a 2023, har yanzu bai riga ya amsa kirar ba," a cewar Eze.


"Siyan fom din takarar shugaban kasa da sunan Dr Jonathan ba tare da izinin sa ba, duba da matsayin da ya rike a kasan nan cin mutunci ne. Don haka ana kira ga al'umma su yi watsi da batun."


Hadakar kungiyoyin arewa ne suka siya wa tsohon shugaban kasar fom din takarar kamar yadda suka sanar da yan jarida a Abuja.


Sanye da huluna 'face kap' dauke da rubutun 'kayi takara Jonathan, kayi takara' mambobin kungiyoyin sun ce Jonathan ne mutumin da ya fi dacewa ya yi takarar shugabancin kasa bayan Muhammadu Buhari.


Tsohon shugaban kasar ya bar wa cikinsa abin da zai yi bayan watsi da tayin da aka masa.


Siyan fom din shine abu na baya-baya da aka yi don janyo hankalinsa ya shiga takarar.


Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.


Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

0 Response to "Jonathan Ya Yi Martani Bayan Ƙungiyar Fulani Ta Siya Masa Fom Ɗin Takarar a APC-BZGLOBALSERVICES"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?