--
Duba wasu manyan cututtuka da yawan cin Suya, Balango, tsire, suke Haifarwa ga Dan adam

Duba wasu manyan cututtuka da yawan cin Suya, Balango, tsire, suke Haifarwa ga Dan adam


Wani masani ilmin kiwon lafiya, Dr. Chinonso Egemba, ya gargadi yan Najeriya kan cin namar Suya da bai gas sosai ba asaboda hakan kan haifar da citar Daji (Kansa). 
Likitan wanda aka fi sani da ‘Aproko Doctor’ a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya yi bayanin cewa akwai sinadarin kemikal dake hawa kan nama irin aka gasa kan hayaki.

A jawabin da ya saki a shafinsa na Instagram @aproko_doctor, yace idan aka gasa kan hayaki, sinadaran hydrocarbon. Yace:

"Idan ka gasa nama a fili, akwai polycyclic aromatic hydrocarbons ko heterocyclic amines. Wadannan sinadarai na haifar da kwayoyin cuta dake lalata DNA, kuma lalacewar DNA na kaiwa ga cutar Daji." "Idan kuma aka gasa naman sosai har wasu bakaken gawayi suka hau kan namar, mutum zai fi saurin kamuwa da cutar daji." 

"An gano cutar dajin ciki, mazakura, da mara na da alaka da wadanann sinadarai." 

"Ku tabbatar da cewa duk naman da zaku ci ba gasawa aka yi ba, zaku iya soyawa ko gasawa a cikin oven." 

A cewar sashen ilmin lafiya ta jami'ar Illinois, 

"Ana samun Polycyclic aromatic hydrocarbon ne idan aka kona abu. Sukan haifar da cutar daji kuma suna illata idanu, koda da hanta." 


 

0 Response to "Duba wasu manyan cututtuka da yawan cin Suya, Balango, tsire, suke Haifarwa ga Dan adam"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?