Yanzu yanzu: Babban Labari Game da Ganin Jinjirin watan Shawwal
A Nigeria - Simwal Usman Jibril yana cikin majalisar da ke kula da sha’anin ganin wata a Najeriya, ya yi bayani a game da haihuwar watan Shawwal.
A wata hira da BBC Hausa ta yi wa da Malam Simwal Usman Jibril a ranar Asabar, ya nuna zai yi wahala a ga jinjirin watan sallah a yammacin yau.
Wannan kwamiti ya na karkashin majalisar koli na harkokin addinin musulunci wanda Mai alfarma Sarkin Musulmi ke jagorantar ayyukanta.
Masanin ya fara da cewa kwamitinsu ya na dogara ne da ganin wata a zahiri kamar yadda addini ya koyar, ya ce ba da lissafin taurari su ke amfani ba.
A tattaunawarsa da ‘yan jarida, ‘dan kwamitin ganin watan ya yi bayani daga Kur’ani kan yadda Ubangiji ya ba ‘Dan Adam ilmin sanin tafiyar wata. Kafin a haifi sabon jinjirin wata a Duniya, masanin ya ce lissafi ya nuna ana daukar kwanaki 29.53.
A lokaci daya ne ake haihuwar sabon wata a duk fadin Duniya. Sai dai kuma kasashe su na samun ganin jinjirin watan ne a lokuta mabanbanta da maraice. Duk da cewa a yammacin yau ne za a zura ido domin neman watan Shawwal, Amma idan aka koma batun ilmin kimiyya, da kamar wuya ya bayyana.
Aikin kwamitin ganin wata shi ne tantance rahotannin da suke samu daga jama’a. Bayan nan kuma sai su sanar da fadar Sultan, Alhaji Sa’ad Abubakar III.
Simwal Jibril ya ce a lokacin da za a gama haihuwar watan gobe a yau, sai kusan karfe 11:28 a kasar Saudi, a Najeriya kuma karfe 9:28 na dare kenan. “Haihuwar sabon watan Shawwal zai faru ne a yau (Asabar), 30 ga watan Afrilu 2022 da kafe 9:28 na dare a Najeriya.” “A wannan mataki, idan wannan ya faru to daga nan ne ake iya ganin jinjirin wata. Za a haifi wata bayan faduwar rana.”
Asali: Legit.ng
0 Response to "Yanzu yanzu: Babban Labari Game da Ganin Jinjirin watan Shawwal "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?