Matashi ya kashe kanin sa da gilashi a kan gajeren wando:- Cikakken Bayani
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi dan shekara 18 mai suna, Abdurahman Sulaiman da zargin cakawa kaninsa fasashen gilashi a ciki ya mutu har lahira.
A naa zargin Sulaiman ya dabawa dan uwansa gialshin ne a wani fada da suka yi da juna da ke cikin birnin jihar Bauchi.
Abdullahi Aminu, wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ya ce, rigima ce ta janyo a ka cakawa kanin gilashi a yayin fadan, sakamakon takaddama kan gajeren wando.
“Marigayin mai shekaru 20 da haihuwa, a na zargin ya bukaci kanensa Abdurahman da ya cire masa gajeren wando da ya ke sanye da ita, wanda ya ce na babban yayansa ne. Kanin ya ki cire shi, sai gardama ta barke, har ta kai ga fada. Kanin ya yi amfani da irin fasashen gilashin nan ya dabawa kanin na sa wuka a ciki, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa,” in Abdullahi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Umar Sanda wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Asabar a Bauchi, ya ce, gardamar ta biyo bayan wani gajeren wando ne da ake zargin na kanin wanda a ke zargin ne.
Kwamishinan ya ce, a halin yanzu wadanda a ke zargin ya na hannunsu, kuma dan uwansa ne na jini a lokacin da babban ya bukace shi da ya cire wando da wanda a ke zargin ya sanya, wanda yayan ya ce nasa ne.
Ya kuma ce, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, inda ya kara da cewa, ‘yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kamo masu aikata irin wadannan miyagun ayyuka. Sannan ya kuma bukaci jama’a da su daina daukar doka a hannunsu.
0 Response to "Matashi ya kashe kanin sa da gilashi a kan gajeren wando:- Cikakken Bayani "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?