--
  [BIdiyo]:- Bayan Jawabin Daurawa Minister Pantami yayi magana akan Mutanen dake Zagin Malamai

[BIdiyo]:- Bayan Jawabin Daurawa Minister Pantami yayi magana akan Mutanen dake Zagin Malamai


 [BIdiyo] Jawabin Minister Pantami akan Mutanen dake Zagin Malamai 


Kamar yanda jawabi ya gabata a baya mai girma Minister sadarwa na Nigeria Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami (Hafizahullah) ya halarci wurin taron bude Masallaci Wanda akayi a jiya a jihar Sokoto 


Inda yazama babban bako me jawabi, kamar godiya ga Allah da salati ga Annabi s.a.w mai girma Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami Ya bayyana irin darajoji da tarin Albarka da alheri da Masallaci keda shi,



Sannan Minister yayi tsokacin sa gameda yanayin da muke ciki musamman wannan al'umma da muke rayuwa a Cikin ta ake samun wadanda basu dauki Malamai da mutunci ba inda wani lokacin har ake samun Wanda zai iya Zagin malami ko Aibata shi,


Hakika maganganun Minister sunja hankali sosai kuma sunyi ma'ana ta yanda ya bayyana wadansu Abubuwa da mutum yakamata yayi a matsayin sadaqatul jariya domin samun tarin lada me yawa




Kadan daga cikin Abubuwa da Minister ya bayyana a matsayin sadaqatul jariya sun hada da Gina Masallaci da kuma samar da ruwa ga Al'umma, muna fatan Allah yasaka da alheri,


Ga Videon domin masu kallo.



0 Response to " [BIdiyo]:- Bayan Jawabin Daurawa Minister Pantami yayi magana akan Mutanen dake Zagin Malamai"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?