Bazawara a Kano ta fasa aure sabo da an kai mata kayan lefe a leda:- Cikakken Bayani
Bazawara a Kano ta fasa aure sabo da an kai mata kayan lefe a leda
Wata bazawara mai ɗa ɗaya ta fasa aurenta bayan da bazawarin da zai aure ta ya aike mata da kayan lefe a ledar bage.
Gidan rediyon Freedom ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a Jihar Kano, bayan da bazawarin, wanda a ka baiyana shi da suna Ibrahim, ya aike da kayan lefen a ledar bage, amma sai ya ga an dawo masa da kayansa.
Da ya ke shaida wa Freedom Radio, bazawarin ya ce sun ɗau lokaci su na soyayya, lamarin da har ya kai ga sun amince da su auri junansu.
Ya ƙara da cewa ganin cewa bazawara ce har da ɗa guda ɗaya, ya ce mata ba zai yi mata lefe ba da wasu gagaruman hidimomi kamar na auren fari ba, amma zai bata kuɗi ta ɗan sayi sabbin kaya, amma sai ta matsa masa cewa sai ya yi mata hidima gagaruma.
Shine shi kuma, a cewarsa, ya sai mata atamfa turmi kala 4 da takalmi, mayafi da kayan shafe-shafe da turaruka, in da ya ƙara da cewa ya kuma bata Naira dubu 30 ta sai wasu abubuwan.
"Amma bayan na kai kayan, kawai sai na ji ta kira ni ta na nuna min bacin ranta. Shine nan take ta nuna min cewa ta fasa auren. Ni kuma na ce a dawo min da kaya na da kuɗi na.
"Da a ka tashi dawo min da kayan, an dawo da su daidai amma a kuɗin an cire naira dubu 10 wai ta yi gyaran jiki da su.
"Gaskiya ban ji dadi ba amma ba komai haka Allah Ya ƙaddara," in ji shi.
Freedom Radio ta sako muryar wata mata da ke haɗa aure, inda ta yi masa alƙawarin ya je ya zaɓi duk wacce ya ke so za a yi musu aure kafin ma watan azumin Ramadana.
0 Response to "Bazawara a Kano ta fasa aure sabo da an kai mata kayan lefe a leda:- Cikakken Bayani"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?