Abin Tausayi:- Yadda Wasu 'yan Mata Suka Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Batsari
Saturday, 19 March 2022
Comment
Yadda Wasu 'yan Mata Suka Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Batsari
Yadda wasu 'yan mata suka kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane a Batsari
Katsina City News
A ranar laraba 15-03-2022, da misalin 12:00am na dare wasu ƴan bundiga suka kai hari Yasu-Yasu wani ƙauye mai nisan 2km daga garin Batsari ta jihar Katsina. Sun bi gida-gida sun ƙwace wayoyin hannu,
kuɗi, suturu da wani ɗan akuya da suka samu a wani gida, sunyi ma mutane dukan tsiya, sannan sun tafi da wasu ƴan mata 2, Mubaraka Naziru da Amina Rabiu.
A hirar da mukayi da su bayan sun kyɓuta daga hannun ƴan bindigai, sun bayyana mana cewa lokacin da suka tafi dasu sun shaida masu cewa su kwantar da hankalin su da sunje wurin oga zaa aurar da su. Sai dai cikin taimakon Allah suna isa dasu maɓoyar tasu,
sai suka kawo masu lemun roba da burodi suma kuma suka sha wasu ƙwayoyi da lemun daga nan barci ya kwashe su.
Gannin haka,
majiyar ta ce yasa ƴan mata suka tashi suka kama hanya cikin salamainin dare suna gudu basu san inda zasu ba,
ga ƙayar sarƙaƙiya da sauran su, inda suka doshi wani tsauni suna tsammanin gari ne amma da isar su suka ga ba haka ba, daga nan suka sake hanya har suka isa rugar wani bafullatani,
Cikin tsoro suka isa gidan suna neman taimako sai yace suyi haƙuri domin sun taɓa taimaka ma wasu aka wulaƙanta su, sai suka nuna masu hanyar Muniya ta ƙaramar hukumar Safana. Suka kama hanya,
da suka isa Muniya suka bayyana halin da suke ciki, sai mutanen gari taimaka masu, inda har wani ya basu tufafin da kuke gani a hoton nan, sannan suka kawo su gida cikin aminci.
A wani kabarin kuma ƴan bindiga sunkai hari ƙauyen Tashar-Nagulle a ranar ta laraba, inda sukna sace dabbobi da babur da suturu, sannan sun bugi matan mutane idan sun tambaye su kuɗi ko wayar hannu, basu samu ba.
0 Response to "Abin Tausayi:- Yadda Wasu 'yan Mata Suka Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Batsari"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?