--
Za'a fara biyan kudin Trader Moni Nan Bada Jimawa ba, Duba Sanarwar Fadar Shugaban Kasa

Za'a fara biyan kudin Trader Moni Nan Bada Jimawa ba, Duba Sanarwar Fadar Shugaban Kasa



Fadar shugaban kasa ta ce shirin nan na Trader Moni na samar da kananan kudade ga kananan ‘yan kasuwa a Najeriya yana nan, kuma zai kai kananan ‘yan kasuwa miliyan 10 a kasar.


Laolu Akande, babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a yammacin Larabar da ta gabata, inda ya ce gwamnati na ci gaba da bayar da lamuni tun bayan da jam’iyyar APC ta lashe zabe.


Ana zargin fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC da sayen kuri’u a fake da sunan Trader Moni, kuma tun bayan cin zabe aka dakatar da shirin.


Sai dai Akande ya ce ba haka lamarin yake ba, inda ya ce sabbin ‘yan kasuwa 30,000 ne suka ci gajiyar kudaden tun bayan kammala zaben.



“Trader Moni, rancen ribar N10,000 kyauta ga kananan ‘yan kasuwa yana kan hanya. Yi watsi da rahotanni sabanin hakan,” in ji Akande


“A gaskiya tun bayan zaben, an ba da rance kusan 30,000 a fadin jihohi goma. Haka kuma tun lokacin da ‘yan kasuwa suka fara biyan Naira 15,000 kuma an fara rabawa kananan ‘yan kasuwa a jihohin Legas da Borno da Ogun da Oyo.


“Ku tuna cewa tare da Trader Moni da zarar an biya N10,000 na farko, dan kasuwan ya sake samun wani N15,000, sannan N20,000 har zuwa rancen N100,000.


“Gwamnatin Buhari ta himmatu wajen aiwatar da wannan shiri kuma a mataki na gaba aiwatar da kananan ‘yan kasuwa miliyan goma na Najeriya za su amfana, wato karin gagarumin kari daga wadanda aka shirya tun farko na miliyan biyu. Kuma wannan na duka Jihohi 36 ne da FCT.



Mataimakin shugaban kasar, wanda ya dauki shirin zuwa manyan kasuwannin kasar nan gabanin zaben, tun daga lokacin da aka kammala zaben ya dakatar da tafiye-tafiye a fadin kasar.



Trader Moni wani tsari ne na karfafawa gwamnatin tarayya ta samar musamman ga kananan ‘yan kasuwa da masu sana’a a fadin Najeriya.


©Ahmed El-rufai Idris


Dandalin wayar da kan matasa na Zumunta na jihar Kaduna.

0 Response to "Za'a fara biyan kudin Trader Moni Nan Bada Jimawa ba, Duba Sanarwar Fadar Shugaban Kasa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?