--
Dalilan da suka sanya Har yanzu ba'a cigaba da tura sakon Training ba Na NYIF ba,  Da fara biyan Kudin NYIF ba, Duba dalilan da Sunday Dare ya Ambata

Dalilan da suka sanya Har yanzu ba'a cigaba da tura sakon Training ba Na NYIF ba, Da fara biyan Kudin NYIF ba, Duba dalilan da Sunday Dare ya Ambata


Ministan wasanni da ci gaban matasa, Sunday Dare, ya bayyana cewa har yanzu ma’aikatar ba ta samu Naira biliyan 25 da aka ware don shirin asusun saka jarin matasa najeriya ba NYIF a shekarar 2021 ba.


Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da bayyani kan kasafin kudin ma’aikatar na shekarar 2021 da kuma kiyasin kasafin 2022 a gaban kwamitin majalisar wakilai kan ci gaban matasa ayau Litinin.


Dare ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan amincewa da naira biliyan 25 na kasafin kudi na shekarar 2021. Sai dai ya ce har yanzu ma’aikatar ba ta yi amfani da kudaden ba saboda wasu dalilai.



Ya ce: “Muna kan wani lokaci da a shirye muke mu samu wannan kudin. Kuma hakan zai zama sanadin kara yawan matasan da za su amfana.


“A yayin da muke magana a yau, CBN ne ya fitar da kudaden da CBN da kuma kananan bankuna ke gudanarwa.


"Suna da dandalin da ke sarrafa shi kuma saboda kudinsu ne, ba mu ba da ko sisin kwabo daga cikin wannan kudin ba."


Ya kara da cewa kimanin ‘yan Najeriya 6,054 ne suka ci gajiyar shirin asusun saka jarin matasa najeriya na Naira biliyan 75, inda ya kara da cewa ma’aikatar za ta kammala 12 daga cikin cibiyoyin ci gaban matasa guda 48 a shiyyoyi shida na siyasa a shekarar 2022.


Ya ce: “A shekarar da ta gabata, za ku tuna cewa shugaban kasa a majalisar ya amince da Naira biliyan 75 na tsawon shekaru uku a karkashin asusun zuba jari na matasan Najeriya.


“Mun fara ne da wani dan karamin rance daga babban bankin Najeriya, CBN.


“Mun nemi Naira biliyan 5 amma kamar yadda muke magana Naira biliyan 2.9 kawai aka saki.


“Yayin da muke magana a yau, 6,054 ne suka ci gajiyar asusun zuba jari na matasan Najeriya.


“Mun ci gaba da tabbatar da cewa gidan yanar gizon mu ya fitar da sunan wasu daga cikin wadanda suka amfana da kudaden da suka karba, bangaren SMEs da suke gudanar da ayyukansu.


“Burinmu shi ne mu tabbatar da cewa mun kara yawan wadanda za su amfana, shi ya sa muka bunkasa a matsayinmu na ma’aikatar tsarin kula da rance.


“Zai ba mu iko dari bisa dari, sannan kuma zai bude mana kofa wajen samun Naira biliyan 25 kai tsaye daga ma’aikatar kudi.


“A shekarar 2022, shirinmu shi ne mu kammala cibiyoyi 12 na ci gaban matasa a shiyyar siyasa.


"Manufar wadannan cibiyoyi na ci gaba shine don kawo ci gaba kai tsaye ga matasa, kiyaye su a cikin al'ummominsu na kusa, inda za su iya koyon fasaha".


©Ahmed El-rufai Idris

Kaduna State Coordinator Zumunta Youth Awareness Forum.

1 Response to "Dalilan da suka sanya Har yanzu ba'a cigaba da tura sakon Training ba Na NYIF ba, Da fara biyan Kudin NYIF ba, Duba dalilan da Sunday Dare ya Ambata"

Tell us what you think about this article?