Sarki ya sa an karbo kayan sa ranar da uban amarya ya ce wakilan ango su koma dasu. duba yadda abun ya faru
Thursday, 2 September 2021
Comment
Daya daga cikin mabiya shafukan sashin Hausa na APA ya turo mana rahoton cewa, mai martaba sarkin Koko ya sa an karbo kayan sa ranar da wasu surukai suka kai a gidan su yarinya a matsayin kayan sa rana inda mahaifin amarya yace wa wakilan angon da su kwashe kayan su tafi da su, su ba zasu wahalar da mai auren yar su ba ga rahoton.
Hukuma ta d’auki matakin da ya dace a kan Wanda ya taka doka, Sannan anje har gidan su yarinyar an karb’o kayan an kuma dawo da su gidan sarki.
Daga nan Kuma sai Sarki yasa a ka cire iya wad’anda doka ta bayar da umarnin yi ga duk wanda ke neman aure,
Daga cikin abunda aka cire su ne.
1_Kwandon goro daya
2_Kwalin biskit daya
3_Kwalin minti daya
4_Da kud’i Dubu biyar.
Ubangiji Allah ya kara taimakon Sarkin Koko da Sarkin Samarin Koko da yan Majalisar Sarkin Samari na Nagarin Koko. Ameeen
Rubutawa.
Dan Malam Koko
0 Response to "Sarki ya sa an karbo kayan sa ranar da uban amarya ya ce wakilan ango su koma dasu. duba yadda abun ya faru"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?