Dubu N20k ake biya AK-47, dubu N5k na harsasai Farsahin yadda ake shigo bindigogi a Yankin Zamfara, Sokoto, Katsina,
Rahotanni sun bayyana yadda 'yan fashin daji ke safarar makamai tsakanin iyakokin Zamfara, Sokoto da Katsina
An gano cewa, ana bai wa mata da yara dubu ashirin na shigowa da AK-47, dubu 5 na harsasai a tsakanin kauyuka Ana alakanta yawon miyagun makaman da harsasai da hadin bakin jami'an da ake baiwa cin hanci a iyakokin kasar nan
Murtala Rufa'i malami ne jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce wani binciken da yayi kan ta'addanci a Zamfara ya bayyana yadda jama'a ke samun kudi daga safarar makamai.
A rahotonsa mai take, "Ni dan bindiga ne": Binciken shekaru 10 kan 'yan fashin daji a jihar Zamfara, Rufai ya ce binciken ya nuna cewa akwai sama da makamai 60,000 a arewa maso yamma, The Cable ta wallafa.
Ya ce kamar makamai kamar bindigogin harbi jirgin sama, abun harba gurneti, AK-47, AK-49, da sauransu duk ana samun su a sansanonin 'yan bindiga a jihar.
Kamar yadda Rufai ya ce, ya tattauna da 'yan bindiga kuma ya ziyarci wasu jihohi inda ya kara da cewa suna samun kudi ta cinikayyar makamai kuma suna kashe kudin ne wurin siyan kwayoyi, neman mata, caca, wayoyi da sauransu.
"Duk wani tushe na samar da makamai ya na yawo ne a bangaren barin iyakokin kasa a bude da kuma gazawar jami'an tsaro wurin toshe dukkan iyakokin kasar nan," rahoton ya ce, wanda aka gabatar a ranar 9 ga Satumba.
“A gaskiya akwai matsalar rashin jami'ai kuma da yawansu sun fi son a kai su iyakokin da ake samun kudi. Sau da yawa ana amfani da kananan iyakokin kasa wurin shigo da makamai."
Ya ce akwai yuwuwar wasu daga cikin jami'an da ke iyakokin ke tayawa tare da taimakawa wurin shigo da makamai cikin kasar nan, The Cable ta ruwaito.
Da yawa daga cikin masu safarar makamai an gano cewa suna amfani da iyakokin Zamfara, Sokoto da na Katsina a yankin arewa maso gabas. "Akwai mata da kananan yara da ake amfani da su wurin shigo da makamai.
Da wuya ake samun mata masu safarar makamai, amma idan aka same su, sun fi kowa iya shigo da makaman.
“Dogaro da nisa da yanayin wurin, ana safarar AK47 a kan N20,000, yayin da harsasai da suka kai 100 ake safarar su kan N5,000 “Safarar harsasan ya fi sauki saboda basu da girma kuma ana iya raba su kashi-kashi, abinda mazauna yankunan ke kira da Geron Hajiya."
0 Response to "Dubu N20k ake biya AK-47, dubu N5k na harsasai Farsahin yadda ake shigo bindigogi a Yankin Zamfara, Sokoto, Katsina, "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?