Maganin Mutuwar Aure: Idan Kana da Aure ko Kina Da Aure Karku wuce batare da kun" Karanta Ba, >>
Kwana 5 ko 8 kafin su fara al’ada suna zama kwanakin hakuri ga duk magidancin da ya gane haka.
Duk da yake cewa ba a cika tattauna irin wadannan abubuwa a nan kasar Hausa ba, amma ya kamata mu fara domin fahimtar juna da rage matsalolin da suke kaiwa ga mutuwar aure.
Na taba karanta cewa mata na fama da wani yanayi mara dadi kafin zuwan jinin al’ada da Bature ke kira da “premenstrual syndrome” (PMS).
Wannan yanayi yakan sa su jin gajiya mai yawan gaske, ko su rika jin fushi kadan-kadan wanda zai iya kaiwa ga kuka kan matsala karama; kuma sukan samun abin da ake cewa “mood swings,” wato canjin yanayi nan da nan, daga farin ciki zuwa bakin ciki.
Wannan yanayin da na ambata a baya da suna PMS din yakan girma ga wadansu matan har ya zama wani yanayi da ake kira PMDD, wato “Premenstrual Dysphoric Disorder”.
Wannan ya fi matsala domin yakan sanya su fishi mai kama da cutar damuwa (depression).
Wani lokacin sukan yi kuka ba gaira ba dalili, ko su shiga damuwa saboda jin cewa kamar kowa ya tsane su, ko kuma su samu kansu a yanayin raguwa ko karuwar son cin abinci, ko rashin jin dadin jiki gaba daya ko ciwon kai ko ciwon mara da ciwon kan mama.
Macen da ke fama da PMDD takan sha wahala kafin tashi daga inda take a kwance ko zaune.
Tana kasa mayar da hankali kan kowane abu, kuma takan yi fushi babu dalili, don haka take fada da kowa har mijinta, taita ihu ga ’ya’yanta ko dalibanta, ko ma tai ta jibgarsu kan laifi dan kadan.
A irin wannan hali, matukar maigida zai ce a’a ga wata bukatarta, to za ta iya kwana tana kuka, kuma za ta iya fada masa komai ya zo bakinta.
Irin wannan ta sa in ka yi aure ake ce maka ka yi hakuri. Nasihar ke nan duk inda ka je!
To babu maganin wannan matsalar?
Gaskiya ni dai ba likita ba ne, amma na karanta wasu shawarwari da likitoci ke bayarwa don rage zafin matsalar.
Likitocin sukan ce wa mace ta sha “antidepressants”, wato magunguna da ke rage damuwa wato “depression”.
Hakana sukan cewa mace ta guji zuwa shagulgulan biki ko shiga cikin mutane a lokacin.
Bugu da kari, a kan ba su shawara da su rika cin abinci mai gina jiki a lokacin tare da yin wasu abubuwa da za su motsa jikinsu wato “edercise” sosai ko iya iyawarsu.
Wannan shawarwari ba ga magidanta kadai suka takaita ba, sako ne har ga iyaye da suke da ’ya’ya matan da aka kasa gane matsalarsu.
Ga wacce ta fahimci tana fama da irin wannan yanayin, to ina ba ta shawara da ta tattauna matsalar da mijinta don fadakar da shi.
Da fata wannan mukala za a amfanar. Mu sha karatu lafiya!
Mubarak Ibrahim Lawan, Malami a Jami’ar Al-Kalam da ke Katsina ne ya rubuto wannan mukala. Za a iya samunsa a abusfyy@gmail.com. 08065462182
Source: Aminya Daily Trust
0 Response to "Maganin Mutuwar Aure: Idan Kana da Aure ko Kina Da Aure Karku wuce batare da kun" Karanta Ba, >>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?