Yara 10 Sun Bakunci Lahira Bayan Cin Tuwon Dawa Duba Karin Bayani>>>
Wasu iyalai 10 sun mutu bayan cin tuwon daya, lamarin da ya girgiza shugaban iyalan Ya shaidawa manema labarai cewa, lamarin ya zo masa ne kamar wasan kwaikwayo Ya kuma bayyana cewa, shi da sauran iyalansa shida ne suka tsira daga wannan bala'i Wani
mahaifin yara 10 da suka mutu bayan sun ci tuwon dawa a kauyen Jangeme, Malam Musa Mai icce, ya ce shi da sauran iyalansa shida ba su ci abincin ba saboda ba sa gida.
Mai icce wanda ya yi magana da jaridar Punch a ranar Asabar ya ce babbar diyarsa ce ta dafa abincin da rana kuma iyalansa 10 suka ci.
"Ni kaina, Rafiatu, Bashar, Babangida, Rabi da Suwaiba ba ma gida." Ya lura cewa dukkan iyalan nasa da sun mutu da kowa yana gida kuma ya ci abincin.
Mai icce ya ce: “Yarinyata ce ta dafa abincin, (tuwon dawa) da rana kuma yara 10 da ke gida suka ci shi yayin da mu shida ba mu nan.
"Wani makwabcina ya kira ni a waya cewa daya daga cikin yara na yana gudawa da amai. Da sauri na dawo gida na kai shi asibiti.
"Lokacin da nake asibiti, an sake kirana cewa sauran yaran sun kamu da gudawa da amai. Na dawo gida na kai su asibiti inda uku daga cikinsu suka mutu da daddare, sauran bakwai kuma suka mutu washegari.
Ya ci gaba da cewa abin da ya faru kamar wasan kwaikwayo ne a gare shi, yana mai jaddada cewa bai taba shiga irin fitinar da ya shiga ba.
A cewarsa: “Na yi matukar girgiza sakamakon bala'in amma na bar wa Allah komai a matsayina na Musulmi. "Ya kasance kamar wasan kwaikwayo a gare ni. Na san ta haka ne aka kaddara ajalinsu.
Mu da ba mu gida a wannan rana ba a kaddara mana mutuwa a lokacin ba. Idan ba haka ba, da mun kasance a gida muma mun ci abincin mun mutu."
0 Response to "Yara 10 Sun Bakunci Lahira Bayan Cin Tuwon Dawa Duba Karin Bayani>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?