--
Yanzu yanzu: Kotu ta bayyana ranar yanke hukuncin Shari'ar  Sheikh Zakzaky Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Yanzu yanzu: Kotu ta bayyana ranar yanke hukuncin Shari'ar Sheikh Zakzaky Da Gwamnatin Jihar Kaduna


 Daga Bilya Hamza Dass


Kotun jihar Kaduna, ta sanya ranar 28/07/2021 domin ta yanke hukunci kan shari'ar Shaikh Zakzaky da gwamnatin jihar Kaduna, wacce ta shafi kimanin shekaru 5 ana gabatarwa. 


Tin a baya de wata babban kotu a babban birnin tarayyan Najeriya Abuja tayi hukunci inda tace ta sallami Shaikh Zakzaky har tayi umurnin da a biya shi diyya tare da gina masa gida a ko'ina yake so. 


Daga bisa ni gwamnatin jihar Kaduna ta sake shigar da karar shi a jihar kan wasu tuhume-tuhume har guda 8 inda take zargin shi da ingiza wasu matasa da sauran su


A zaman da akayi yau wanda shi ne na ƙarshe, lauyan Shaikh Ibraheem Zakzaky Mr. Femi Falana (SAN) ya bayyana cewa “Ya ce dukkan wadanda aka zarga da kashe Kofur Yakubu Dankaduna an gabatar da su a gaban wannan kotu kuma kotu ta sallamesu. Ya ce tunda kotun nan ta sallami wadanda aka zarga da kisan ta yaya za a hukunta wanda ake zargin taimaka musu kawai ya yi?


Ya ce maganar tare hanya kuma ko taro ba bisa izini ba, shima wani abu ne da ya kamata kotu ta sami cewa ba zai shafi wanda ake kara ba. 


Kuma maganar tare hanya shima ba yadda za a jingina shi da Malam. Domin an kama wadanda ake zargi kuma an gabatar da shaidu dukkansu ba wanda ya jingina wannan tare hanya ga wanda ake kara na farko” in ji shi


Amma lauyan gwamnati Barista Dari ya ce ana iya hukunta wanda ya taimaka aka aikata laifi ko da an saki wanda ya aikata laifi din. Dari ya nemi kotu da ta yi watsi da no case submission da aka shigar a gabanta.


Barrister Enegedu, wanda shi ne yake wakilntan Malama Zeenat ya bayyana cewa dukkan shaidun da aka gabatar a gaban kotu ba wanda ya alakanta Malama Zeenat da dukkan laifuka 8 da ake zargin aikatawa. Ya bayyana cewa dukkan wadanda suka ba da shaida ba su kira sunan Malama ba. Tun daga tare hanya a ranar 12/12/2015 gar zuwa ranar 15/12/2016.


Bayan kotun ta gama sauraron duka bangarorin Lauyoyin ta sanya ranar 28/07/2021 domin yanke hukunci kan shari'ar.

0 Response to "Yanzu yanzu: Kotu ta bayyana ranar yanke hukuncin Shari'ar Sheikh Zakzaky Da Gwamnatin Jihar Kaduna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?