--
Kalli Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

Kalli Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano





"An harbi wanda ake zargin a kafarsa na dama a yayin da ya yi kokarin tserewa, an garzaya da shi babban asibitin Doguwa an masa magani. 


An kwato bindiga pistol a hannunsa da waya Tecno da sim kad da yayi amfani da shi wurin yi wa wanda ya yi korafin barazana, adda da leda (wanda zai saka kudin fansan a ciki.)" 


Kakakin yan sandan ya kara da cewa a ranar 2 ga watan Yuli, tawagar yan sanda yayin sintiri a dajin Falgore karamar hukumar Tudun Wada sun kama wani Abdulrahman Usman na kauyen Kurmi a karamar hukumar Soba na jihar Kaduna da wasu mutane 5 da suka kai hari rugar makiyaya a dajin. 


"Makiyayan sun dakile harin suka yi wa maharin rauni, sannan daga bisani yan sanda suka kama shi dauke da pistol na gargajiya," in ji shi. 

















An garzaya da shi asibiti aka masa magani sannan daga bisani ya tona asirin abokansa da dama da suke aikata laifuka tare. Ya kuma amsa cewa sun aikata fashi da makami da garkuwa da mutane sau da dama. 


Kakakin yan sandan ya ce an kama wani Rabiu Danjuma da aka fi sani da Rabiu Duty; Suleiman Idris, wanda ake fi sani da Magu; Abel Patrick, Wisdom John da Stephen Sedani. 


Ya ce wadanda ake zargin sun kai hari gidan wani Sahaisu Abdullahi mazaunin kauyen Gunduwawa a karamar hukumar Gezawa suka sace masa mitarsa, Honda Accord da Talabijin. 


An kuma kama wani Abdullahi Ibrahim na Gidan Kankara Quaters a Kano wanda ya hada baki da wani Bashir Bashir wanda aka fi sani da Sahabi; suka kaiwa daliban FCE Zaria hari suka kwace musu wayoyin salula da kudinsu ya kai N200,000. 


"Yan sandan sun kuma kama wani Khalifa Muhammad, Ahmed Muhammad da Halifa Ahmed duk mazauna kurna Quaters dauke da bindigan roba, kakin sojoji, wayoyin salula, kudi da wasu kayayyaki. 


"Yayin bincike sun amsa cewa sun yi wa wata Hajiya Umma Musa fashi sun mata rauni. Ana cigaba da bincike," in ji shi. 


Kazalika, an kuma kama mutane 37 da ake zargi masu kwacen waya ne a Kogar Dan'agundi. "A ranar 04/06/2021 misalin karfe 7 a yamma, yan sanda sun samu rahoton cewa wasu bata gari dauke da adduna, wukake da wasu muggan makamai suna tare mutane a Kofar Dan'agundi suna kwace musu wayoyi, kudade da wasu kayayyakin. 


"Nan take kwamishinan yan sandan Kano, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko, fsi, ya tra tawaga karkashin jagorancin SP Bashir Gwadabe domin a kamo su." 


Da isarsu, bata garin sunyi kokarin kai musu hari amma yan sandan suka yi galaba kansu, hakan yasa suka bar makamansu suka tsunduma cikin kududufin Bakar Lamba a Kofar Dan Agundi amma yan sandan suka zagaye kududufin suka kama su. An kama kimanin mutum 37 daga cikinsu tare da kwato makamai da muggan kwayoyi da suke dauke da su. 










Related Posts

0 Response to "Kalli Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?