FG Ta Sake Kara Wa'adin Hada Layin Waya da NIN, Ta Fadi Dalili>>>
Gwamnatin tarayya ta sake kara wa'adin haɗa layin waya (SIM) da lamabar katin ɗan kasa (NIN) har zuwa 31 ga watan Oktoba, karo na shida tun watan Disamban shekarar da ta gabata.
A wani jawabin haɗin guiwa da hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta fitar a shafinta na Facebook, ranar Lahadi, ya nuna cewa an ɗauki wannan matakin ne biyo bayan roƙon masu ruwa da tsaki domin shirin yakai har kananan yankuna, yan ƙasashen waje da kuma yan Najeriya dake ƙasashen duniya.
Jawabin wanda ke ɗauke da sanya hannun kakakin NCC, Ikechukwu Adinde, da takwaransa na NIMC, Kayode Adegoke, ya nuna cewa karin wa'adin zai magance karancin rijista a makarantu da asibitoci, kamar yadda kididdiga ta bayyana.
Wani sashin jawabin yace: "An ɗauki matakin ne biyo bayan nazari kan cigaban da ake samu kan shirin na haɗa SIM-NIN a faɗin ƙasar nan."
"Zuwa ranar Asabar 24 ga watan Yuli, akwai na'urorin yin rijista 5,500 a ciki da wajen ƙasar nan domin saukaka wa mutane wajen rijistar NIN da kuma haɗa lambar da SIM."
Shugaba Buhari ya amince da karin
Jawabin ya ƙara da cewa gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta amince da karin wa'adin a kokarinta na sukakawa yan Najeriya dake ciki da wajen ƙasa. Hakanan kuma domin saukaka wa mazauna ƙasar a bisa doka su mallaki lambar NIN ta hanyar amfani da damar karin wa'adin.
Kusan mutun 60 miliyan sun mallaki NIN Jawabin yace: "Zuwa yanzun yan Najeriya kimanin miliyan 59.8m sun yi rijistar NIN, tare da haɗa layukan waya 3-4 kowace lamabar."
"Bisa adadi mai yawa na cibiyoyin rijista a ciki da wajen ƙasa da kuma wasu da za'a ƙara nan gaba, kowane ɗan Najeriya da wanda doka ta basu damar zama zasu samu damar mallakar NIN."
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, a madadin FG, ya yaba wa gwamnatin jihar Kano da wasu jihohi, waɗanda suka maida NIN wajibi ga masu sha'awar shiga makarantu.
Pantami ya yaba wa yan Najeriya bisa hakurin da suka nuna da juriya wajen biyayya ga umarnin gwamnatin tarayya na haɗa SIM-NIN. Hakazalika gwamnatin tarayya ta bayyana jin daɗinta kan rahoton cewa amfani da NIN a jarabar hukumar JAMB ya rage ƙalubalen satar jarabawa.
0 Response to "FG Ta Sake Kara Wa'adin Hada Layin Waya da NIN, Ta Fadi Dalili>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?