Duba Muhimman abubuwa 10 da suka faru yau agurin mukabala da Abduljabbar>>>
Bayan jiran watanni da aka yi, an gudanar da muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu malamai a Jihar Kano ranar Asabar, 10 ga watan Yulin 2021 wadda gwamnatin jihar ta shirya.
'Yan jarida ƙalilan ne suka shiga ɗakin muƙabalar ciki har da wakilin BBC Hausa a Kano Khalifa Shehu Dokaji. Jami'an tsaro sun yi wa ofishin Hukumar Shari'a ta Kano tsinke, wurin da aka gudanar da muhawarar.
Waɗannan abubuwa da za ku karanta ba su ne baki ɗayan abubuwan da suka faru yayin muƙabalar ba. Kuna iya shiga wannan shafin domin samun ƙarin bayani,
Sharuɗan da aka ce za a yi amfani da su yayin gudanar da muƙabalar
Kafin tsunduma cikin muhawarar gadangadan, alƙalin muƙabala Farfesa Salisu Shehu - shugaban cibiyar Musulunci da tattaunawa tsakanin addinai ta Jami'ar Bayero - ya bayyana sharuɗa kamar haka:
Za a bai wa dukkan ɓangarorin dama ba tare da fifita wani ba
Za a bai wa kowane bangare minti 10
Dukkan maudu'i suna da minti 30 tare da bayar da min 5 na ɗauraya
Za a bayar da dama na minti 5 na nuna hoto ko bidiyo ko sauti
Ba a yarda masu muƙabala su katse ɗaya daga cikinsu ba yayin da yake magana har sai lokacin da aka bayar ya cika
Ana buƙatar hujjoji ingantattu kuma karɓaɓbu a Musulunci
Dolo ne dukkan masu muƙabalar su kiyaye cakuɗa hadisai da ayoyi, a gabatar da su cikin ladabi
Dole ne a girmama juna tare da yin amfani da lafazi na mutuntawa
Babu zuga babu kirari, ko wani abu da zai nuna ɓangaranci
Malaman da suka fafata da Abduljabbar
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya fuskanci malamai huɗu ne yayin muƙabalar domin kare kansa daga zargin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.
Malam Mas'ud Mas'ud Hotoro daga ɓangaren ɗariƙar Ƙadiriyya kuma tsohon ɗalibin Sheikh Abduljabbar
Malam Abubakar Mai Madatai daga ɓangaren Tijjaniyya
Mallam Kabir Bashir Kofar Wambai daga ɓangaren ƙungiyar Izala
Dr. Muhammad Rabiu Umar Rijiyar Lemo daga ɓangaren Salafiyya
Ba zan tuba ba - Sheikh Abduljabbar
Shehin malami Abduljabbar Nasiru Kabara wanda shi ne mai kare kansa daga malamai huɗu da ke zargin da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW, ya ce ba zai tuba ba a wurin wannan muƙabala "saboda rashin ƙwararan hujjoji".
Ya faɗi hakan ne a daidai loacin da Mallam Abubakar Madatai ya ce duk wanda ya ci mutuncin Annabi hukuncinsa kisa ne sannan ya nemi Abduljabbar da ya fito fili ya tuba.
Sai malamin ya ce: "Ba zan tuba a wurin wannan mukabala ba har sai an ba ni cikakkiyar hujja. Indai aka ba ni hujjojin da suka fi nawa zan tuba, amma yanzu mutum ba zai tuba ba bayan yana kan gaskiya. Ba'a biyo turbar da zan tuba ba."
Ina roƙon a sake yin muƙabala - Sheikh Abduljabbar
Malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya roƙi 'yan uwan muhawararsa da gwamnatin Kano mai shirya muƙabalar da a asake zaman yin tattaunawa jim kaɗan bayan Mallam Abubakar Madatai ya tambaye shi game da cewa Annabi SAW ɗan giya ne.
Mallam Abubakar Madatai: "A wane hadisi ne ya zo cewa Annabi ɗan giya ne?; Lokacin da aka yi aurensa da Nana Khadija da a buge aka yi shi saboda sun sha giya; Annabi ya fito daga tsatson da ba tsarkakakke ba."
Abduljabbar: "Abu ne mai sauki; ji ne ko dai ma'anar ce ba a fahimta ba. Dukkan kalaman da ake tuhumata a kai kore su nake yi daga Annabi SAW. Ina roƙon a sake saka rana don sake tattaunawa da waɗan nan malamai don fito da abubuwa."
Minti 10 sun yi kaɗan wajen kwance litattafan da na zo da su - Abduljabbar
Sheikh Abduljabbar ya ce shi ma Annabi yake karewa daga irin ƙagen da ake yi masa a wasu hadisai amma babu isasshen lokaci na tabbatar da hakan "saboda minti 10 sun yi kaɗan".
"Abin da nake yi nake yi ina yin su ne don rarrabe hadisan da ake yi wa Annabi ƙarya. Da don Annabi ake yi da an bayar da isasshen lokaci don a yi muƙabalar. Littafan da na zo da su, minti goma sun yi kaɗan a kwance su.
0 Response to "Duba Muhimman abubuwa 10 da suka faru yau agurin mukabala da Abduljabbar>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?