Duba Magunguna 10 da citta ke yi a jikin dan adam musamman ma'aurata>>>
Duk dai da cewar anfi sanin itacen citta da yaji “Ginger” a turance, amma wannan yajin yanada matukara amfani a jikin mutun.
Hakan yasa wasu masana sun gudanar da bincike akan irin magunguna da itacen citta keyi, musamman wajen bada lafiya mai nagarta ga mutane idan har anyi amfani da ita ta hanyar da suka kamata.
Kwararrun likitoci a yankin kasashen Asia, sun bayyanar da wasu magunguna guda goma, da itacen citta keyi.
1. Sukace idan mutun nasamu matsalar narkewan abinci a cikin shi to citta zata yi masa magani.
2. Citta na magani ga mace mai juna biyu dake yawan amai.
3. Citta na maganin jiri da kasalar jiki ga mace mai juna biyu.
4. Kana idan mutun na fama da cutar Sankara, yana iya amfani da citta wajen jinyar cutar.
5. Iccen citta anyi ittifakin cewar yana da karfin da yake yakar wasu kananan cuttutuka da suke yawo a cikin jinin mutun.
6. Haka itacen citta kan kara dumin jikin mutun wanda hakan zai sa jini ya dinga gudana yadda yakamata a kowane lokaci.
7. Likitocin suka kara da cewar duk mutumin da ya rike amfani da citta to lallai zai samu lafiya mai nagarta.
8. Citta bata tsaya kawai a lafiyar ciki ba, har ma da yaki da cuttutuka da suke addabar mutane wajen kamuwa da mura da ma wasu cuttutka da sukan kama fatar mutun.
9. A bincike da aka gudanar da yayi nuni da cewar citta na taimakawa wajen rage maikon da bashi da amfani a jikin mutun.
10. Haka idan mutun na fama da ciwon gabobi, yayawaita amfani da citta wanda zata taimaka mishi so sai wajen samun lafiya.
Kuyi Share Zuwa ga Sauran Al-ummah Domin Amfanarsu!
0 Response to "Duba Magunguna 10 da citta ke yi a jikin dan adam musamman ma'aurata>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?