--
Yanzu yanzu: JAMB Ta Fidda Sabuwar Sanarwa Kan Ranar Rufe Rajistar Jarrabawar Shekarar 2021

Yanzu yanzu: JAMB Ta Fidda Sabuwar Sanarwa Kan Ranar Rufe Rajistar Jarrabawar Shekarar 2021


Hukumar jarrabawa ta JAMB ta fitar da sabuwar sanarwa kan halin da ake ciki na jarrabawar,  


Hukumar ta ce ta tura masu son rubuta jarrabawar zuwa cibiyoyin rubuta jarrabawar ta sakon tes Hakazalika hukumar ta bayyana cewa, wadanda basu kara rajistarsu su kara zuwa ranar Talata, 


Hadaddiyar Hukumar Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta yi kira ga masu neman shiga makarantu da aka tantance su da su kammala rajistar jarrabawar ta 2021 zuwa ranar Talata. 


Dr Fabian Benjamin, Shugaban yada labarai na JAMB, ya yi wannan kiran ne a madadin kungiyar jarabawar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Channels Tv ta ruwaito. 


Ya lura cewa JAMB ta tsawaita wa'adin yin rajistar da wasu makwanni biyu zuwa ranar 29 ga Mayu bayan wa'adin da aka tsara tun farko don rajistar 2021/2022 UTME / DE ta kare a ranar 15 ga Mayu. 


Jarrabawar wacce aka shirya yinta tsakanin 5 ga Yuni zuwa 19 ga Yuni an maida ita yanzu za ta fara daga 19 ga Yuni zuwa 3 ga Yuli. 


Ya bayyana cewa an kara karin makonni biyu ne domin tattara jerin sunayen dukkan masu son rubuta jarrabawar da suka kasa yin rajista. 


Ya kara da cewa, “An tura sunan cibiyar rajista ga kowane mai son rubuta jarrabawa ta hanyar sakonnin GSM (SMS) kuma akwai shi a shafin yanar gizon hukumar (www.jamb.gov.ng) daga karfe 12 na rana a ranar Litinin, 14 ga Yuni , 2021.”


Kakakin JAMB din ya sanar da masu son rubuta jarrabawar cewa an yi amfani da lambar tantancewa na kan kowane fom don tura su zuwa cibiyoyin rajistarsu. 


A cewarsa, masu son rubuta jarrabawar da suka amintar da bayanan su ne ake sa ran za su ziyarci cibiyoyin. Hakazalika "Kowane mai son rubuta jarrabawar da aka tura zuwa wata cibiyar, 


CBT da ba mallakar JAMB ba ana sa ran zai biya kudin rajista na N1,000 ga cibiyar ta CBT," in ji shi, The Guardian ta ruwaito. 


Source: Legit

DAGA: BZ NEWS 24/7

0 Response to "Yanzu yanzu: JAMB Ta Fidda Sabuwar Sanarwa Kan Ranar Rufe Rajistar Jarrabawar Shekarar 2021"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?