
Yanzu yanzu: INEC Ta Soke Wasu Runfunan Zaɓe 746 a Faɗin Najeriya
Wednesday, 16 June 2021
Comment
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta soke wasu runfunan zaɓe 746 dake faɗin Najeriya,
waɗanda mafi yawancin su a wurin bauta, gidan sarauta da kuma wuri mai zaman kanshi suke, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shine ya faɗi haka ranar Laraba a Abuja, a wurin taron da hukumar ke gudanarwa da kwamishinonin zaɓe RECs.
Daga runfunan zaɓen 119, 973 da ake da su, Farfesa Yakubu yace yanzun akwai runfunan zaɓe 176, 846 a faɗin Najeriya, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Shugaban INEC ɗin yace an samu wannan ƙarin ne bayan wata kwaskwarima da hukumar ta gudanar a faɗin runfunan zaɓen dake ƙasar nan.
Cikakken bayani zai zo daga baya
Source: Legit
DAGA BZ NEWS 24/7
0 Response to "Yanzu yanzu: INEC Ta Soke Wasu Runfunan Zaɓe 746 a Faɗin Najeriya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?