--
Yanda Hukumar SSS ta cika hannu da mawakin daya soki Annabi (S.a.w) a kano

Yanda Hukumar SSS ta cika hannu da mawakin daya soki Annabi (S.a.w) a kano


Hukumar SSS ta cafke wani mawaki da ya rera wata wakar data soki mutuncin Annabi Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa, ta karbi korafe-korafe kan wakar mara dadin ji SSS ta ce mawakin ya nuna nadama ya kuma nemi gafarar al'ummar musulmi baki daya 


Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ta sake cafke wani mawaki mai suna Ahmad Abdul, a kan wata waka da ake jin ta soki Annabi kuma za ta iya haifar da rudani a jihar Kano. 


Jami'an SSS din sun ce sun dauki Abdul ne a hannun jami'an tsaro don kauce wa mummunan abinda zai faru dashi daga mazauna Kano, Premium Times ta ruwaito. 


Yayin da yake tsare, Abdul ya nemi gafarar daukacin al'ummar musulmi, gwamnatin jihar Kano da malaman addinin Islama. Ya gaya wa SSS cewa bai gane cewa wakar ta saba wa koyarwar Musulunci ba.


Da yake tsokaci, Sakataren zartarwa na Hukumar Tantancewa ta Jihar Kano, Ismaila Afakallah, ya ce ya karbi daruruwan korafe-korafe a kan wakar daga ‘yan jihar.


Afakallah ya ce ya kai karar mawakin ga jami’an SSS wadanda suka cafke shi a wani otal da ya boye tsawon kwanaki. Mahaifin mawakin, Abdullahi Isa, ya gode wa hukumar ta SSS saboda dauke matakin da ta yi a kan lokaci wanda ya kauce wa barkewar doka da oda. 

0 Response to "Yanda Hukumar SSS ta cika hannu da mawakin daya soki Annabi (S.a.w) a kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?