--
Wata Sabuwa: Matsalar Tsaro ta Ta'azzara, An Umarci Bokaye Su Dauki Mataki

Wata Sabuwa: Matsalar Tsaro ta Ta'azzara, An Umarci Bokaye Su Dauki Mataki


Domin magance matsalar tsaro a wasu sassan kudancin Najeriya, gwamna ya ba bokaye umarnin daukar mataki 


Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya ce bokaye su nemo hanyar da za ta magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta 


Ba wannan ne farko ba, tuni wata jihar Kudu maso gabas ta fara aiki da kambun tsafi domin magance matsalar tsaro 


Gwamnatin jihar Oyo da ke kudancin Najeriya ta bai wa bokayen da ke jihar umarnin su dauki kowane irin mataki domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar. 


Legit.ng Hausa ta ruwaito ta BBC na cewa, kwamishinan Yada Labarai na jihar, Dr Wasiu Olatunbosun ne ya bayar da umarnin ga kungiyar masu maganin gargajiya ta jihar a madadin Gwamna Seyi Makinde na Oyo.


Ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ba su dukkan goyon bayan da suke bukata domin taimakawa wajen samar da maganin matsalar tsaro. 


Matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta karade kowane yanki na Najeriya, ciki har da yankin kudu maso yamma inda kabilar Yarabawa ke da rinjaye mai yawa. 


Hakazalika, yankin na fuskantar rikicin manoma da makiyaya kari a kan kungiyoyi masu fafutikar ballewa daga Najeriya da nufin kafa kasar Yarabawa ta Oduduwa. 

0 Response to "Wata Sabuwa: Matsalar Tsaro ta Ta'azzara, An Umarci Bokaye Su Dauki Mataki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?