--
Twitter ta rubutowa FG wasika, tana bukatar a tattauna kan dakatar da ita,

Twitter ta rubutowa FG wasika, tana bukatar a tattauna kan dakatar da ita,


Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa Twitter ta zo mata da bukatar zama a yi sasanci Kamar yadda ministan yada labarai da al'adu, 


Lai Mohammed yace, dama can kofa bude take Mohammed yace dole ne Twitter ta yi rijista da NBC kuma ta kiyaye abubuwan da za a dinga wallafawa, 


Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta tabbatar da cewa Twitter ta rubuto mata wasika da bukatar tattaunawa kan matsalolin da suka sa gwamnatin ta dakatar da ita. 


Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya tabbatar da hakan yayin da ya bayyana a shirin "siyasar kasa baki daya", 


wani shirin gidan rediyon Najeriya ne da Kamfanin Dillancin Labarai ya kiyaye a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito. 


"Ina tabbatar muku da cewa Twitter ta yi wa gwamnatin tarayya wasika na cewa ta shirya tattaunawa. "Kamar yadda muka ce, kofa a bude take amma sai Twitter ta yi abinda ya dace," yace. 


Ministan ya jaddada matsayar gwamnati na cewa ba za ta lamuncewa kowacce irin kafar sada zumunta ba da zata taimaka wurin tarwatsa kasar nan. 


Mohammed ya ce daga cikin sharuddan dawowar Twitter Najeriya shine dole ne a yi yarjejeniya kan abinda za a iya wallafawa.


Yace Twitter da sauran kafafen sada zumunta dole ne su yi rijista tare da samun lasisi daga NBC kuma su kiyaye sharuddan lasisin tare da biyan haraji, rahoton NNN.


Kamar yadda ministan yace, sanya dokokin kafafen sada zumunta al'ada ce ta kowacce kasa a duniya. 


Ya ce kasashe da yawa yanzu sun gano cewa kafafen suna karfi fiye da gwamnati kuma dole ne a saka musu sharuddan. 


"Singapore, Algeria, Pakistan, Turkey duk suna da dokokin kiyaye kafafen sada zumunta, Australia haka. 


"Hatta EU da bata da wasu dokoki dangane da kafafen sada zumunta ta yi haka a rubuce," yace 


Source: Legit

DAGA: BZ NEWS 24/7

0 Response to "Twitter ta rubutowa FG wasika, tana bukatar a tattauna kan dakatar da ita, "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?