--
Subahanallah: Ana zaman makoki a Zamfara

Subahanallah: Ana zaman makoki a Zamfara


na can su na ci gaba da makoki bayan kisan gillar da 'yan fashin daji suka yi wa mutane a cikin gonakinsu.





Da yammacin ranar Laraba, wani shaida ya ce sun yi wa mutum goma sha bakwai, jana'iza kuma an raunata ƙarin manoma tara, baya ga dabbobi da suka yi awon gaba da su.





Manoman na tsaka da aikin share gonakinsu lokacin da maharan suka auka musu.





Wani da ya tsallake rijiya da baya a harin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa sun yi jana'izar mutanen da aka hallaka.





Sannan ƴan bindiga sun wawushe musu dukiya da dabobbi. Kuma babu jami'in tsaro lokacin da aka kai musu harin.





BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin SP Muhammad Shehu, jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sandan jihar Zamfara, sai dai haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.





Rahotun BBC




0 Response to "Subahanallah: Ana zaman makoki a Zamfara"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?