--
Muna buqatar ayi gwajin miyagun kwayoyi tamkar na HIV kafin Aure - Hukumar NDLEA

Muna buqatar ayi gwajin miyagun kwayoyi tamkar na HIV kafin Aure - Hukumar NDLEA


Shugaban hukumar NDLEA ya bayyana bukatar yi wa mutane gwajin shan kwayoyi kafin a yi aure 


Ya bayyana haka ne da nufin rage shaye-shaye da ke addabar al'umma Najeriya cikin shekarun nan 


Hakazalika ya bayyana adadin da ake samu na masu shan miyagun kwayoyi a cikin al'ummar Najeriya Janar Buba Marwa (mai ritaya), shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ya bayyana bukatar gwajin shan miyagun kwayoyi kafin a yi aure kamar yadda ake na HIV. 


Buba Marwa ya fadi hakan ne a wata hira da BBC Hausa albarkacin ranar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyo Ta Duniya da ake yi duk ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara. 


Yayin da yake zantawa, Marwa ya ce: "A kasar nan, mutum daya cikin bakwai, yana shaye-shaye. Majalisar dinkin duniya a kowace shekara tana zaban rana daya, wanda duniya za ta hade a yi jawabi kuma a nemi mafita game da shaye-shaye a duniya baki daya.


Ya kuma ta'allaka tashe-tashen hankula da yawaitar sace daliban makaranta dake faruwa a kasar da shan miyagun kwayoyi. Hakazalika, ya ce game da auren dan shaye-shaye: "Me yasa idan ana gwajin HIV, Genotype kafin a yi aure, me ya hana a yi shan miyagun kwayoyi shima? Dole mu fito da wasu hanyoyi." 

0 Response to "Muna buqatar ayi gwajin miyagun kwayoyi tamkar na HIV kafin Aure - Hukumar NDLEA"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?