
'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika
Mutanen Olopa Estate a jihar Osun sun tsinci wata wasika da ke cewa yan fashi za su kawo musu ziyara Wasikar wadda aka rubuta da yarbanci da turanci ta ce su tara N20m su bawa mai unguwa ya ajiye wa barayin idan ba su son a ziyarci gidan kowa
Hukumar tsaro ta Amotekun ta ce ta samu labarin wasikar amma tana ganin cika baki ne duk da haka ta tsaurara matakan tsaro Mutanen unguwar Olopa Estate da ke Ofatedo a karamar hukumar Egbedore a jijar Osun suna zaman dar-dar bayan samun wata wasika da ke cewa yan fashi za su zo unguwar sata,
Vanguard ta ruwaito. A cikin wasikar wanda aka rubuta wani sashinsa da harshen yarabanci, an umurci mutanen unguwar su tara Naira miliyan 20 su bawa mai unguwa ya ajiye wa yan fashin idan ba su son a bi su gida-gida.
Wasikar ta ce: "Sanarwa, muna son sanar da ku cewa mu barayi muna nan zuwa mu yi fashi a kowanne gida a unguwarku ko kuma ku tara Naira miliyan 20 ke bawa mai unguwa mu tafi wurinsa mu karba idan mun zo.
"Za mu zo da karfinmu kuma za mu kashe dukkan masu tsaronku idan suka ce za su dame mu." Abinda mazauna unguwar suka ce game da wasikar
Wani mazaunin unguwar, Tejumade Adewale ya ce wasikar ya janyo rudani sosai a unguwar har ta kai ga wasu sun dena kwanciya a gidajensu.
Duk da haka, an karo yan banga, wasu mutanen su kan zo ne kawai da rana su dauki wani abu su koma shagonsu su kwana. "Muna kira ga jami'an tsaro su zo su taimaka mana kuma kada a yi wasa da barazanar," in ji shi.
Matakin da Amotekun ta dauka Sahara Reporters ta ruwaito cewa Kwamandan Amoketun na Osun, Kwamared Amitolu Shittu ya ce hukumar ta san da batun wasikar kuma ta shirya wa 'bakin'.
Ya kara da cewa barazanar ba wani abu bane amma duk da haka an tanadi jami'an tsaro don dakile harin. "Mun ji barazanar, muna ganin cika baki ne kawai, duk da haka, an tsaurara matakan tsaro a unguwar don gudun bacin rana," in ji shi.
0 Response to " 'Ku tara N20m ku bawa mai unguwa, muna nan zuwa', Ƴan fashi sun aikawa mutanen unguwa wasika"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?