--
 Kalli Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita

Kalli Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita


Ahmad Ibrahim Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya auri kyakyawar amarya Shuwa Arab mai suna Zainab Algoni Abdulwahid 


An yi bikin a sirrance ba tare da gagarumin taro ba a ranar Juma'a domin gujewa cece-kucen jama'a Zukekiyar amarya Zainab za ta koma Abuja daga Maiduguri a ranar Lahadi kamar yadda majiya mai karfi ta sanar 


Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan yayi sabuwar amarya a sirrance a wani biki da ba a tara jama'a ba a jihar Borno. 


SaharaReporters ta tattaro cewa sunan amaryar shugaban majalisar dattawan Zainab Algoni Abdulwahid, matashiyar budurwar Shuwa Arab 


SaharaReporters ta ruwaito cewa an yi bikin ne a sirrance domin gujewar cece-kucen jama'a yayin da amarya Zainab za ta koma Abuja a ranar Lahadi. 


Wani kwarya-kwaryan walima aka yi a gidan amaryar dake lamba 1, Gwange, layin Malut Shuwa dake Maiduguri. 



"Shugaban majalisar dattawan Najeriya ya auri matashiyar budurwar Shuwa Arab a Maiduguri. Sunanta Zainab Algoni Abdulwahid.


"An daura musu auren ne bayan sallar Juma'a a Maiduguri. Amaryar zata kama hanyar Abuja zuwa ranar Lahadi. "An yi bikin an sirrance ne. 


Shugaban majalisar dattawan bai halarci daurin auren ba amma ya tura wakilai kuma sun je har an daura. 


"Amma amaryar tayi shagalin bikinta a gidansu dake Gwange, titin Malut Shuwa dake Maiduguri," majiyar ta sanar da SaharaReporters.



A yayin da aka tuntubi Ola Awoniyi, mai bada shawara na musamman ga shugaban majalisar dattawan kan yada labarai, ya ce yana filin sauka da tashin jiragen sama. Bayan an tura masa sakon kar ta kwana, bai yi martani a kai ba. 

0 Response to " Kalli Hotunan zukekiyar Shuwa Arab da Sanata Ahmed Lawan yayi wuff da ita "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?