Duba yadda Kwastam ta kama tabar wiwi ta fiye da Naira Miliyan 91 ɓoye a motar yashi a Legas
Wata motar yashi makare da tabar wiwi ta shiga a Jihar Lagos An kiyasta kudin tabar kusan fiye da kimanin naira miliyan 91 An boye tabar data kai sinki dubu uku cikin buhi 41 a tsakiyar yashi cikin wata tifa,
Jami'an hukumar Kwastam reshen Seme ta bankado sinki 3,186 na tabar wiwi da aka ɓoye a cikin tifa dauke da yashi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Sinkin wiwin, wanda aka ɗaure a akalla buhu 41 a cikin tifa an kama ta ne a titin Seme-Badagry, an ƙiyasta kudin ta zai kai kimanin naira miliyan 91,488,977.
The Cable ta ruwaito cewa Abdullahi Hussain, mai magana da yawun Kwastam shiyyar Seme, a wata sanarwa ranar Laraba, ya ce an kama tifar da safiyar Talata, bayan bayanan sirri da suka samu.
A rahoton NAN, an binciki motar, kuma an gano buhi 41 ɗauke da sinki 3,186 na tabar wiwi, da shaidar da biyan kuɗi kimanin N91,488,977.
Abdullahi ya kara da cewa Bello Jibo, shugaban shiyyar Seme na Kwastam, ya yaba da aikin tare da karfafa mu su gwiwa wajen zakulo ayyukan bata gari a fadin ƙasa.
Ya kuma roki jami'an da su hada kai da mutanen gari, don samun goyon bayan su wajen gudanar da aikin su.
0 Response to "Duba yadda Kwastam ta kama tabar wiwi ta fiye da Naira Miliyan 91 ɓoye a motar yashi a Legas"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?