
Da dumi-dumi: PDP ta rasa mambobinta 2 a majalisar wakilai, sun sauya sheka zuwa APC
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta rasa mambobinta biyu a majalisar wakilai ta tarayya
'Yan majalisar daga jihar Cross Ribas, Lego Idagbo da Michael Etiaba sun sauya sheka zuwa APC a ranar Talata, 29 ga watan Yuni Sun bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a PDP a jihar su a matsayin dalilin ficewar su
Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar wakilai sun nuna adawa ga sauya shekar wasu mambobin jam’iyyar zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki,
a ranar Talata, 29 ga watan Yuni. Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Toby Okechukwu, da wasu sun yi adawa da sauya shekar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Cross Ribas, Lego Idagbo da Michael Etiaba, wanda aka sanar yayin zaman majalisar na yau Talata.
Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da sauya shekar a zaman majalisar inda ya ce 'yan majalisar biyu sun fice daga PDP sun koma APC, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Dukansu sun bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a PDP a jihar su a matsayin dalilin ficewar su, jaridar The Cable ta ruwaito.
Sai dai kuma, mambobin na PDP sun ce sauya shekarsu ya saba wa doka. Okechukwu ya bayyana cewa majalisar ta kara wasu jerin karya doka ta hanyar karbar sauya shekar nasu.
Gbajabiamila, ya yi ikirarin cewa mambobin PDP ba su da ikon tantance yanayin sauya shekarsu, yana mai cewa kotu ce kawai za ta iya yin hakan.
0 Response to " Da dumi-dumi: PDP ta rasa mambobinta 2 a majalisar wakilai, sun sauya sheka zuwa APC "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?