--
Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu,

Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu,


Wata amarya da angonta sun janyowa kansu maganganu da tambayoyi a kafar sada zumunta bayan bidiyon bikinsu ya bazu Ma'auratan 


an ga suna ciyar da juna tare da shayar da juna yayin da suke nuna tsabar bakin cikinsu duk da ranar aurensu ce Sau da yawa bikin aure yana kasancewa mai dadi kuma ma'aurata na nun zumudinsu yayin da ake bikinsu amma wannan daban ne 


Wasu masoya biyu da suka angonce sun janyo maganganu a kafar sada zumunta kan yadda suka ciyar da juna tare da shayarwa yayin liyafar bikinsu. 


A wani bidiyo da @gossipboyz1 suka wallafa a Instagram, an ga ma'auratan suna yi wa juna kallon tsana da hantara a ranar bikinsu a maimakon murmushi yayin ciyar da juna.


An ji bakin dake wurin suna tsokaci yayin da ma'auratan ke nuna tsana ga junansu. Angon ne ya fara ciyar da amaryar da kek yayin da itama ta bashi. 


Sun sake maimatawa da ruwa inda ya bata, itama amarya ta bashi dukkansu rai a bace. Su waye wadannan ma'auratan? 


Legit.ng ta kasa gano su waye ma'auratan nan saboda wanda ya wallafa bidiyon a Instagram bai bada wani karin bayani ba bayan tsokacin da ya saka karkashin bidiyon. Kamar yadda aka saka a kasan bidiyon: "Kalla tashin hankali a ko ina." 


Me jama'a ke cewa? Ma'abota amfani da Instagram sun cika sashin tsokaci da abinda ke ransu. 


@tessy_diamond ta ce: "Gidan sauro ne ta saka a kanta?" 


@hideezbeautypro tsokaci tayi da cewa: "Wannan fuskar amaryar tawa ce?" 


@irabor.faith rubutawa yayi: "Amma yanayin kek din yayi kyau, sai dai ban san abinda yasa suke bakin ciki ba" 


@favour091 cewa tayi: "Me yasa basu murmushi ne?" 


Source: Legit

BZ NEWS 24/7

0 Response to "Bidiyon amarya da ango suna yi wa juna kallon tsana yayin liyafar bikinsu ya janyo maganganu, "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?