--
Anzo wajen: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

Anzo wajen: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja


Masu zanga-zangan neman Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus wato 'Buhari Must Go' sun sake yin zanga-zanga a Abuja 


A wannan karon sun yi zanga-zangan ne a safiyar ranar Litinin inda suka cinna wuta a titin Musa Yar'Adua Way da ake bi zuwa filin tashin jiragen sama 


Masu zanga-zangar na rike da takardu da ke dauke da kokensu da kuma dalilan da yasa suke son shugaban kasar ya yi murabus 


Wasu masu zanga-zanga a Umaru Yar'Adua Way, babban birnin tarayya Abuja, a safiyar ranar Litinin sun banka wuta a kan titi, hakan ya janyo cinkoson ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito. 


Titin na Musa Yar'Adua Way ne ake bi idan za a tafi filin tashi da saukan jiragen sama a birnin tarayyar Abuja.


The Cable ta ruwaito cewa masu zanga-zangar suna ta ihu cewa 'Buhari Must Go' ma'ana 'Dole Buhari Ya Tafi' yayin da suke dauke da takardu masu rubutu daban-daban na nuna rashin kaunar kasancewar shugaban kasar a kan mulki. 


Masu motoci da sauran ababen hawa sun rika yin dabaru suna kaucewa wutar da aka kunna a tsakiyar titin. A shekarar bara an taba yin zanga-zanga makamancin wannan a ranar June 12 inda aka kama da yawa cikin masu zanga-zangar. 


Omoyele Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa kuma mai jagorancin yan zanga-zangar #RevolutionNow, daga bisani ya wallafa hotuna da bidiyon masu zanga-zangar a shafukansa na sada zumunta. 


Abin da masu zanga-zangan ke bukata Masu zanga-zangar suna neman gwamnati ta kawo karshen kallubalen rashin tsaro, mulki mara kyau, saba doka ba tare da hukunci ba, janye dakatarwar da gwamnati ta yi wa shafi Twitter da wasu matsaloli da suka lissafa a takardun da suke dauke da su.


Zanga-zangar na Buhari Must Go ya ja hankulan mutane da dama a yankunan kasar tare da neman Shugaban kasa ya yi murabus musamman a lokacin da hare-haren yan bindiga da satar mutane don kudin fansa ke yawaita. 

0 Response to "Anzo wajen: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?