Yanzu yanzu: Saudiyya tayiwa Isra'ila babban martani, duba matakin data dauka
Kasar Saudiyya da Masar sun bukaci a dakata da luguden wuta tsakanin Isra'ila da Falasdin
Kasashen biyu sun bayyana rashin jin dadinsu ga yadda lamarin ke kara ta'azzara a yanzu
Saudiyya ta bukaci jami'an diflomasiyya da su tinkari Isra'ila kan kisan gilla ga Falasdinawa Ministocin harkokin wajen Masar da Saudiyya na kira da a tsagaita wuta nan take a fadan da a ke tsakanin Isra’ila da Hamas a Zirin Gaza,
Al Arabiya ta ruwaito. Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa a ranar Asabar wacce kamfanin dillacin labarai na Saudiyya ya fitar.
Sanarwar ta ce Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya yi magana da Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry.
Ta kuma bayyana, dukkansu sun amince cewa ana bukatar tsagaita wuta nan take.
Misira na ta kokarin sasantawa don dakatar da fadan. Sanarwar ta Saudiyya ta kuma ce jami'an diflomasiyyar biyu sun yi kira ga
"gamayyar kasa da kasa da su tinkari munanan ayyukan da Isra'ila ke yi wa al'ummar Falasdinawa 'yan uwansu."
Source: Legit
0 Response to "Yanzu yanzu: Saudiyya tayiwa Isra'ila babban martani, duba matakin data dauka"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?