--
Yanzu-yanzu: Isra'ila ta rusa ofishin gidan jaridar Aljazeera dake
Gaza, Falasdin

Yanzu-yanzu: Isra'ila ta rusa ofishin gidan jaridar Aljazeera dake Gaza, Falasdin


Kasar Isra'ila ta kai hari gidan benen da ofishin gidan jaridar AlJazeera, AP da wasu kamfanonin jaridar ke ciki a birnin Gaza, kasar Falasdin.





A bidiyon da Alarabiya ta dauka, an ga yadda makami mai linzami da Isra'ila ta harba ya rusa ginin har kasa.





Mai ginin benen, Jawwad Mahdi, ya bayyana cewa hukumar Sojin Isra'ila ta kirashi cewa za'a kaiwa gidansa hari.





Ya bayyana cewa an fada masa ya sanar da wadanda ke cikin ginin su tattara inasu-inasu su bari cikin awa guda.





Kalli bidiyon:








Source: Legit




0 Response to "Yanzu-yanzu: Isra'ila ta rusa ofishin gidan jaridar Aljazeera dake Gaza, Falasdin"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?