--
Yanzu yanzu: ICPC Ta Fara Farautar Sirikin Buhari Ruwa a Jallo

Yanzu yanzu: ICPC Ta Fara Farautar Sirikin Buhari Ruwa a Jallo


Hukumar yaki da rashawa ta ICPC na neman, Gimba Kumo, sirikin Shugaba Buhari da wasu mutum biyu ruwa a jallo





A sakon da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta ce ana zargin mutanen uku ne da ɓannatar da kudade da karkatar da $65m





Hukumar ta yi kira ga mutane su kai rahoto hedkwatar ta da ke Abuja ko jihohi ko ofishin ƴan sanda idan suna da bayani mai amfani kansu,





Hukumar yaki da rashawa ta ICPC na ta ayyana Gimba Yau Kumo, surukin Shugaba Muhammadu Buhari ruwa a jallo kan zargin damfara ta $66m, The Cable ta ruwaito.





A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, Azuka Ogugua, mai magana da yawun hukumar ya ce ana neman Kumo da Tarry Rufus da Bola,





Ogunsola ruwa a jallo kan zargin ɓannatar da karkatar da kudaden shirin samar da gidaje na ƙasa.





Kumo, tsohon shugaban Bankin Samar da Gidaje na Nigeria, ya auri, Fatima, ƴar shugaban ƙasa a 2016 a Daura, jihar Katsina.





"Hukumar yaki da rashawa ta ICPC na neman mutane uku da aka saka hotunansu ruwa a jallo, Mr Gimba Yau Kumo,





Mr Tarry Rufus da Mr Bola Ogunsola kan ɓannatar da kuɗi na Hukumar Samar da Gidaje na Ƙasa da karkatar da Fam miliyan 65 ($65,000,000), a cewar ICPC.





"Duk wani da ke da bayani mai amfani game da su ya kai rahoto hedkwatar ICPC da ke Abuja ko kuma duk wani ofishin ICPC na jihohi ko ofishin yan sanda mafi kusa."





A watan Afrilu, kwamitin majalisar dattijai na binciken yadda ake kashe kudaden gwamnati ta gayyaci Kumo domin ya yi bayani zargin rashin ƙa'ida da aka bi wurin bada kwangilar Naira biliyan 3 a lokacin da ya ke bankin.





Source: Legit




0 Response to "Yanzu yanzu: ICPC Ta Fara Farautar Sirikin Buhari Ruwa a Jallo"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?