--
Kalli Bidiyon fasto tana tsinewa 'yan cocinta a kan sun ki tara mata
kudin Birthday

Kalli Bidiyon fasto tana tsinewa 'yan cocinta a kan sun ki tara mata kudin Birthday


Wata fasto mace ta zage mambobin cocinta da tsinuwa bayan sun ki tara mata kudin shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta





Faston da ta bayyana wani bidiyon da ke yawo a kafar sada zumunta, an ji tana kiran mambobin cocinta da shaidanu saboda makon da suka nuna mata





An ji tana cewa ba amfanin kanta za ta yi da kudin ba, su za ta hadawa abincin da zasu ci saboda wasu daga cikinsu kamar aladu suke





Wata fasto ta yi tofin Allah tsine ga mambobin cocinta sakamakon kin tara mata kudin shagalin murnar bikin zagayowar ranar haihuwarta da suka yi.





A wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an ji faston tana kiran mambobin cocinta da shaidanu saboda kin yi mata wannan kara da suka yi.





"Ko a ranar zagayowar haihuwata, wasu daga cikinku sun ki bada kudi. Ubangiji zai ladabtar da ku saboda baku da tausayi, sai dai kuma idan baku da kudin."





"Ba wai kamar kudin nawa bane, na abincin da zaku zo ku ci ne. Wasu daga cikinku mugun ci garesu kamar aladu kuma sai kun kwasa wani abincin kun tafi da shi gida," faston tace.





Ga bidiyon nan mai karatu ya kalla a kasa:








Source:legit




0 Response to "Kalli Bidiyon fasto tana tsinewa 'yan cocinta a kan sun ki tara mata kudin Birthday"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?