Iyaye sun yi kira da a canza lokacin haska shirin Dadin Kowa
Mutane a jihar Kano sun bayyana damuwarsu kan shirin wasan kwaikwayo na Dadin-Kowa Iyaye sun yi kira ga a dakatad da shirin Dadin-kowa a watan Ramadana saboda yana daukewa 'yayansu hankali daga ayyukan ibada, musamman Sallah.
Sun ce yaransu na wasa da Sallah musamman ranakun Talata da Asabar da ake haska shirin a tashar Arewa24.
A cewarsu, lokacin shirin ya zo daidai da lokacin Sallan Isha'i da Taraweeh kuma hakan na hana wasu yara da manya Sallah.
A rahoton da Daily Trust ta tattara, wata majiya ta bayyana cewa gidan Talabijin na Arewa24 ta kasa canza lokacin saboda ba tashar yan Najeriya bace.
"Gudun kada a ragewa masu masu kallon Arewa24 dake wajen Najeriya, ba za'a iya canza lokacin ba," majiyar tace.
Iyayen sun yi kira ga shugabannin tashar da su canza lokacin saboda 'yayansu su mayar da hankali kan ayyukan ibada a watan Ramadana.
Daya daga cikin iyaye, Hajiya Amina, ta bayyanawa DT cewa, "Za mu so shugabannin tashar su duba lokacin shirin a watan Ramadana.
Wannan shirin na hana yara zuwa Masallaci." Wani mahaifin, Alhaji Ali Mohammed yace: "Wasu lokutan sai na kashe Talabijin na korasu Masallaci.
Sun fi mayar da hankali kan shirin fiye Sallar Isha'i da Taraweeh a wannan watar." l
Source: Legit.ng
0 Response to "Iyaye sun yi kira da a canza lokacin haska shirin Dadin Kowa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?