--
Gwamnatin Tarayya za ta shigar da mutane 3000 a gaban kotu saboda
taurin biyan bashin N5tr

Gwamnatin Tarayya za ta shigar da mutane 3000 a gaban kotu saboda taurin biyan bashin N5tr


Hukumar Asset Management Corporation of Nigeria mai kula da kadarorin gwamnatin tarayya tana shirin shiga kotu da wasu mutane a kasar nan.





Jaridar Punch ta ce kusan mutum 3000 ake bi makukun bashi da har yau sun gagara biya, don haka hukumar AMCON ta yanke hukuncin zuwa kotu.





AMCON ta bayyana wannan mataki da ta dauka ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Mayu, 2021, bayan wani taron kara wa juna sani da aka shirya a garin Legas.





A jawabin da hukumar ta AMCON ta fitar a jiya, ta ce akwai kadarori kusan 6, 000 a bankuna da mutane kimanin 3, 000 suka bada jingina, suka karbi bashi.





AMCON ta ce yayin da wadannan kadarori ke ajiye, wadannan mutane ba su cika alkawarin da aka yi da su na cewa za su biya bashin gwamnatin kasar ba.





Shugaban AMCON na kasa, Ahmed Kuru, ya ce shekara biyar kenan da suka shigo da tsarin AMP, an yi nasarar karbo wasu dukiyar gwamnati da suka makale.





Hukumar ta ce wannan tsari zai taimaka wajen gabatar da kara a kotu a fadin kasar nan. Jaridar The Nation ta ce AMCON ta nemi agajin sauran abokan aikinta.





A cewar hukumar AMCON, tana kokarin karbo fiye da Naira tiriliyan biyar da mutane suka karba a matsayin bashi, amma suka gagara maida wadannan kudin.





Mutane 350 kacal ake bin fiye da 80% na bashin da aka gaza biya, adadin kudin da wadannan daidaikun mutane suka gagara biya ya kai Naira tiriliyan 3.6.





Da ace an karbo wadannan kudi, za su isa a gina abubuwan more rayuwa irinsu tituna, hanyar jirgin kasa, ko a inganta wutar lantarki, da habaka kiwon lafiya.





Source: Legit




0 Response to "Gwamnatin Tarayya za ta shigar da mutane 3000 a gaban kotu saboda taurin biyan bashin N5tr"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?