Daga karshe Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da fasahar 5G
Daga karshe, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a fara amfani da fasahar 5G
Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka saka hannu tsakanin NCC da Nigcomsat
Kamar yadda aka tabbatar, kaddamar da fasahar a kasar nan zata kawo kudin shiga ga FG Daga bisani, cece-kucen da ke tattare da fasahar 5G ta zo karshe bayan gwamnatin tarayya ta kammala shirin rungumar fasahar.
Wannan ya biyo bayan saka hannu kan wata yarjejeniya tsakanin hukumar sadarwa ta kasa (NCC) a ranar Laraba da kuma hukumar sadarwa ta tauraron dan Adam (Nigcomsat).
Vanguard ta ruwaito cewa, a karkashin yarjejeniyar, NIGOSAT zata zuba 160Megs na C-Band wanda gwamnati za ta samu kudin shiga daga siyar dashi ga kamfanonin sadarwa ta karkashin NCC.
Yarjejeniyar kamar yadda mataimakin shugaban NCC, Farfesa Umar Danbatta, ta samu sa albarkar National Frequency Management Council, wanda ya samu shugabancin Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami.
A bangaren cece-kucen dake tattare da fasahar 5G, EVC tace tuni ta yi bincike a bangaren tsaro da kuma lafiya kuma hukumar ta bazama wurin wayarwa jama'a kai. Tun dai a farkon 2020 ne maganar fasahar 5G ta janyo cece-kuce a kasar nan.
Source: Legit
0 Response to "Daga karshe Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da fasahar 5G"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?