--
Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana
Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu

Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu


Gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnatin Kaduna da shugabannin ƙungiyar ƙwadugo zuwa wajen taron sulhu a Abuja FG ta shirya taron ne a ƙoƙarin da take yi na samar da maslaha a tsakanin ɓangarorin biyu





Za'a yi taron ranar Alhamis 20 ga watan Mayu a ofishin ministan ƙwadugo na ƙasa dake babban birnin tarayya, Abuja Gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, da shugabannin NLC zuwa wajen taron gaggawa data shirya domin yin sulhu a tsakanin su, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.





Gwamnatin ta sanya ranar Alhamis 20 ga watan Mayu domin tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin biyu a babban Birnin tarayya Abuja.





Wannan na cikin ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi domin dakatar da yajin aiki da kuma rikicin dake tsakanin gwamnatin Kaduna da ƙungiyar kwaduga kan sallamar ma'aikata a jihar Kaduna. Gwamnatin ta gayyaci ɓangarorin biyu ne ta ofishin ministan kwadugo,





Chris Ngige, domin ta shiga tsakani, kamar yadda The Nation ta ruwaito. An shirya yin zaman sulhun ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a ofishin ministan kwadugo na ƙasa ranar Alhamis a Abuja.





Waɗanda aka gayyata zuwa wajen taron sulhun sun haɗa da; Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i tare da manyan jami'an gwamnatinsa, da kuma shugaban NLC, Ayuba Waba, tare da manyan shugabannin ƙungiyar.





SOURCE: LEGIT






0 Response to "Da Ɗumi-Ɗumi: FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?