
Da duminsa: Kalli Bidiyon Yanda Yan Sanda Suka Harbi Sowore a Abuja
Monday, 31 May 2021
Comment
Yan sanda a babban birnin Tarayya Abuja sun harbi mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma tsohon dan takarar shugaban kasa yayin wata zanga-zanga a bakin Unity Fountain dake a Abuja.
An harbi Sowore a gefen dama a cinya lamarin da ya sa aka yi gaggawan wucewa dashi asibiti.
Ya rubuta a shafin Tuwita:
"Yanzun nan 'yar sanda, ACP Atine ta harbe ni a Unity Fountain a Abuja. #RevolutionNow Yanzu aka fara gwagwarmaya za ta ci gaba koda kuwa za su dauki raina!"
Kalli Bidiyon Yanda abun ya faru a qasa:
— IBILIBEOGADA % (@Nija_4life) May 31, 2021
Source: Legit
0 Response to "Da duminsa: Kalli Bidiyon Yanda Yan Sanda Suka Harbi Sowore a Abuja"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?