--
Da duminsa: Gwamnatin tarayya takara wa'addin kule layukan waya

Da duminsa: Gwamnatin tarayya takara wa'addin kule layukan waya


Ƙarin wa'adin ya biyo bayan wata ganawa da Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya yi da shugabannin hukumar sadarwa ta NCC da kuma hukumar samar da lambar NIN wato NIMC.





Sanarwar da kakakin hukumar NCC da na ma'aikatar sadarwa suka fitar ta ce an ɗauki matakin ƙara wa'adin zuwa 30 ga Yuni saboda buƙatar da mahukunta suka nuna ta cewa hakan zai bai wa 'yan ƙasa damar yin rajistar cikin sauƙi.





"An samu gagarumin ci gaba a rajistar haɗa NIN da layukan waya," a cewar sanarwar.





"Kusan mutum miliyan 54 ne suke da lambar NIN a yanzu, abin da ke nufin masu amfani da layin waya kusan miliyan 190 kenan tun da bincike ya nuna cewa kowace lambar NIN na ɗauke da layukan waya uku zuwa huɗu."





Sanarwar ta ƙara da cewa kamfanonin sadarwa da sauran cibiyoyin hukumar NIMC sun sake buɗe sabbin wuraren rajistar domin bai wa mutane da dama damar yi.





Gwamnatin Najeriya ta ce haɗa layukan waya da lambar ɗan ƙasa ta NIN zai inganta tsaro da kuma bayanan da take da su na 'yan ƙasa baki ɗaya, yayin da ake ƙara wa lambar muhimmanci a wuraren ayyukan gwamnati a kowane mataki.





Source: BBC hausa








0 Response to "Da duminsa: Gwamnatin tarayya takara wa'addin kule layukan waya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?