--
Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada ranakun Laraba da Alhamis hutun
Sallah

Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada ranakun Laraba da Alhamis hutun Sallah


Gwamnatin tarayya ta bada ranakun Laraba da Alhamis daidai da 12 da 13 ga watan Mayun 2021 a matsayin hutun sallah





Ministan al'amuran cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a garin Abuja





Yayi kira ga 'yan Najeriya dake gida da ketare da su yi amfani da wannan damar wurin addu'ar zaman lafiya a fadin kasar nan





Gwamnatin tarayya ta bayyana Laraba, 12 da Alhamis 13 ga watan Mayun 2021 a matsayin hutun sallah karama mai zuwa.





Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bada wannan sanarwar a madadin gwamnatin tarayya a Abuja a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.





Ya taya Musulmi murnar zuwan sallah tare da kira ga 'yan Najeriya dake gida da ketare da su yi amfani da wannan lokacin wurin yin addu'ar zaman lafiya, daidaituwa da kuma habakar tattalin arzikin kasar nan.





A wata takarda da Aregbesola ya fitar kuma sakataren ma'aikatarsa, Dr Shuaib Belgore yasa hannu, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kasance masu bin doka tare da kaunar juna, juriya, hakuri da ladabi kamar yadda Annabi Muhammad ya koyar.





Ya yi kira ga hukumomin tsaron kasar nan da su kasance masu jajircewa da kishin kasa a yayin da suke yaki da barkewar rashin tsaro da sauran al'amuran ta'addanci dake faruwa a kasar nan.





Ya tabbatar da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kawo karshen wannan barkewar ta'addancin kuma za ta dawo da zaman lafiya a kowanne sako da lungun kasar nan.





Source: Legit




0 Response to "Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada ranakun Laraba da Alhamis hutun Sallah"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?