--
Da dumi duminsa: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Saki Mai Ɗakinsa Melinda

Da dumi duminsa: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Saki Mai Ɗakinsa Melinda


Bill Gates, attajirin duniya kuma wanda ya kafa kamfanin kwamfuta na Microsoft ya sanar da shirinsa na rabuwa da mai dakinsa Belinda.





Bill da Melinda sun sanar da labarin ne a shafukansu na Twitter a ranar Litinin inda suka ce sun dauki wannan matakin ne bayan nazari sosai.





Yayin aurensu na tsawon shekaru 27, sun haifi yara uku. "Bayan nazari mai zurfi da aiki kan zaman aurenmu, mun cimma matsayar kawo karshen auren," a cewar sanarwar.





A cikin shekaru 27 da suka gabata, mun haifi yara uku sannan mun kafa gidauniya da ke ayyuka a sassan duniya domin inganta rayuwan mutane.





"Za mu cigaba da aiki tare domin cimma wannan manufar a gidauniyarmu amma ba za mu iya cigaba da kasancewa ma'aurata a yayin da za mu shiga matakai na gaba a rayuwarmu.





"Muna rokon a bamu sarari tare da mutunta sirrinmu a yayin da iyalin mu ke shiga wannan sabon rayuwar."








Source: Legit




0 Response to "Da dumi duminsa: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Saki Mai Ɗakinsa Melinda"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?