--
Cikin daren jiya 'Yan Bindiga Sun Sace Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar
Katsina

Cikin daren jiya 'Yan Bindiga Sun Sace Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar Katsina


Wasu 'yan bindiga sun afkawa masallaci a jihar Katsina, inda suka sace mutane sama 40





An ruwaito cewa, sun shigo ne cikin dare suka sace masallatan yayin da suke sallar Tahajjud





Shaidu sun ce 'yan bindigan ba su yi harbi ba yayin harin har sai da suka gama sannan suka tsere Akalla mutane 40 ne ‘yan bindiga suka sace a yayin da suke gudanar da sallar Tahajjud a wani masallaci da ke garin Jibiya na jihar Katsina.





Mazauna garin sun shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa ‘yan bindiga da dama sun kai hari a masallacin da misalin karfe 2 na daren Litinin kuma suka tafi da masu ibadar.





An tattaro cewa masu garkuwan da farko sun dauki mutane 47, ciki harda mata da yara, amma daga baya bakwai suka dawo.





"Ya zuwa yanzu mutane 40 ne suka bata bayan harin," in ji wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa.





Wani mazaunin garin da ya bayyana haka, Lawal Jibiya, ya ce mazauna kauyukan sun sanar da su game da harin, bayan sun ga motsin 'yan bindigar da ke kan hanyar zuwa garin.





Ya ce daruruwan matasa da kungiyar 'yan banga da ke cikin garin suna cikin shirin ko ta kwana don tunkarar 'yan ta'addan, amma maharan suka sauya hanyarsu suka shiga garin daga mashigar yamma.





“Muna tsammanin su daga mashigar gabas ta hanyar Daddara, Kukar Babangida ko Magama amma a wannan karon sun wuce bayan gari suka yada zango a Jibawa.





"Daga Jibawa daga nan suka zagaya zuwa mashigar yamma kusa da asibitin Yunusa Dantauri kuma suka far wa wani masallaci a bayan gari," in ji shaidar.





A cewarsa, 'yan bindigan ba su yi harbi ko daya ba har sai da suka gama barnarsu. Jibiya, wani gari ne da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Nijar, na daya daga cikin wuraren da ake yawan yin garkuwa da mutane da kuma yawaitar barnar ‘yan bindiga.





Source: Legit




0 Response to "Cikin daren jiya 'Yan Bindiga Sun Sace Masu Sallar Tahajjud 40 a Jihar Katsina"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?