Bincike nanuna za'ayi ambaliya a jihohi 28 A Najeriya bana, Duba Jihohin Anan>>>
Ana hasashen mumunan ambaliyar ruwan sama a jihohin Najeriya akalla 28 a bana, sabon rahoton hasashen ambaliya AFO ya nuna. Ana fitar da wannan rahoto ne a kowani shekara.
Jihohin da aka lissafo sune,:
Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano and Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara.
Ministan arzikin ruwa, Suleiman Adamu, ya lissafa wadannan jihohi ne ranar Alhamis a taron gabatar da rahoton hasashen ambaliya na shekara-shekara na hukumar ayyukan ruwa a Najeriya (NIHSA), rahoton Daily Trust.
"Wannan shekarar, zamu yi fama da matsaloli guda biyu; na COVID-19 da kuma ambaliyar ruwa kamar yadda akayi hasashe," yace. "A takaice, rahoton AFO na 2021 ya nuna cewa kananan hukumar 302 a jihohin Najeriya da birnin tarayya ake sa ran fuskantar ambaliya."
"Jihohin dake makwabtaka da tekun Niger da Benue ko shakka babu za'ayi mumunan ambaliya." Ministan ya ce saboda haka suka shirya don ankarar da yan Najeriya kan abinda ka iya faruwa. Ya yi kira ga yan Najeriya su taimakawa wadanda wannan iftila'i ya fadama wa.
Source: Legit.ng
0 Response to "Bincike nanuna za'ayi ambaliya a jihohi 28 A Najeriya bana, Duba Jihohin Anan>>>"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?